El-Rufa\’i Ya Ziyarci Sheikh Algarkawee Da \’Yan Bindiga Suka Sace Kwanakin

0
561

 

Daga Usman Nasidi

A RANAR Laraba ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa\’i ya ziyarci babban malamin addinin Islama, Sheikh Adam Algarkawee, da \’yan bindiga suka sace kwanakin baya tare da wasu almajiransa.

An saki makamin ne bayan biyan kudin fansa, miliyan N10m, kamar yadda majiyar mu ta tabbatar.

A ranar Alhamis ne wasu yan bindiga da suka yi awon gaba da fitaccen Malamin addinin Musunluncin nan dake zaune a jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Al-Garkawy tare da wasu dalibansa.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun yi garkuwa da shehin Malamin tare da dalibansa ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Agusta, a daidai lokacin da suka kai ziyara gonar makarantarsa dake gefen garin Kaduna.

Duk da irin kokarin da gwamnatin tarayya take yi game da yaki da masu garkuwa da mutane a Najeriya, amma ayyukansu na cigaba da ta’azzara a yankin Arewa maso yamma, musamman ma a jihar Kaduna, lamarin da yafi shafar al’ummar garin Birnin Gwari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here