Na Yafewa Duk Wadanda Suka Gana Min Azaba Ta Tsawon Shekara 15 – Al-Mustapha

0
497

 

Daga Usman Nasidi

 

MANJO Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin tsohon shugabn kasar Najeriya a mulkin soji, marigay Janar Sani Abacha, ya bayyana cewar ya yafewa dukkan masu hannu cikin ukubar da aka shafe shekara 15 ana gana masa.

An kama tare da tsare Al-Mustapha ne bisa zarginsa da kisan Kudirat Abiola, uwargidan mutumin da ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 1993, marigayi Moshood Abiola.

Da yake jawabi a wani taro na kungiyoyin Kiristoci fiye da 40, Al-Mustapha, ya bayyana cewar ya yafewa kafatanin masu hannu a daurin da aka yi masa.

A cewar Al-Mustapha, sau 11 ana yunkurin hallaka shi a kan laifin da bai san komai a kai ba amma Allah yana kubutar da shi.

Sannan ya kara da cewar akwai wasu muhimman bayanai da ya samu a kan kungiyar Boko Haram lokacin da yake gidan yari tare da bayyana cewar wasu ‘yan boko ne suka kirkiri kungiyar.

“Sun kawo ‘yan Boko Haram 138 dakin da nake a gidan yari, bayanan da suka sanar da nib a zan iya fadawa ‘yan Najeriya ba saboda dalilan tsaro” a cewar Al-Mustapha.

Hakazalika ya bayyana cewar an kirkiri rikicin makiyaya da manoma dagan-gan domin kawar da hankalin ‘yan Najeriya daga wasu abubuwa dake faruwa a kasa. Sai dai bai bayyana ko wadanne abubuwa ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here