A YI BABBAR SALLAH RANAR TALATA A NIJERIYA  DAIDAI NE-SHEIKH SA’IDU JINGIR

0
1568
Sheikh Sa\'idu Hassan Jingir;

 Isah  Ahmed, Jos

 SA\’I na kasa kuma mataimakin shugaban majalisar  malamai na biyu  na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah ta kasa,  Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya bayyana cewa yin babbar sallah ranar talata a Nijeriya dai dai ne, domin za a yi hawan Arfa  ne a ranar litinin. Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce makkah ita ce cibiyar musulunci ta duniya kuma ba zai  yiwuwa ba, ace  an yi Arfa yau limamin duniya ya yi huxuba kuma  an gayawa musulmi cewa yau ranar Arfa ce wato 9 ga wata,  gobe  ranar idin babbar sallah. Sannan a wayi gari wata kasa da take da’awar musulunci,  su ce ba za su yi aiki da wannan sanarwa ba.

Sheikh Sa’idu Jingir ya yi bayanin cewa wani abu ne ake samu a kasarmu Nijeriya, wanda  idan aka samu labarin cewa Saudiya sun ga wata, mu kuma nan Nijeriya sai a yi fatawa da ka.

Ya ce mun sha tattauna wadannan abubuwa a wuraren tarurrukan da muke yi a Nijeriya. Mun ja hankalinsu kan cewa a ka’idar shari’a idan aka ce gabashin duniya ta ga wata, to yammacin duniya duk wadanda labari ya riske su, za su yi lissafi da wannan ganin wata.

‘’Tilas  ne mu bi lissafin Saudiya mu yi watsi da lissafin kasarmu. Saboda haka sai mu yi idin babbar sallah a ranar talata washe garin ranar litinin  an yi Arfa na duniya. Wanda kuma Allah ya ba su iko su yi azumin ranar Arfa. Wanda azumin ranar Arfa nan, Manzon Allah SAW ya ce yana kankare zunubi na shekara guda da watanni shidda ga wanda bai sami tafiya aikin hajji ba. Kaga bai yiwuwa a ce za mu canja lissafi ya kasance ba mu sami yin wannan azumi ba. Wannan al’amari yana nan yadda yake abin da Nijeriya ta yi na cewa a yi sallah ranar Talata ya yi daidai’’.

Sheikh Sa’idu Hassan ya bada tabbacin cewa idan suka je Saudiya aikin hajji, tun da yanzu suna kan hanya  zasu yi magana da hukumomi a can kan wannan al’amari. K uma idan Allah ya ba su ikon dawowa gida Nijeriya. Bayan sallah za su kai ziyara ga mai alfarma Sarkin musulmi su jawo hankali cewa  a kirawo malamai a zo a zauna a tattauna a kawo mafita kan wannan al’amari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here