‘Yan Nijeriya Ku Zabar Wa Buhari ‘Yan Majalisa Masu Kishi-Dokta Nasiru Usman Isah Ahmed, Jos Mataimakin Darakta Janar na makarantar horar da lauyoyi ta Nijeriya da ke Kano, kuma malami a makarantar koyar da dabarun mulki da ke Kuru a Jos, Dokta Nasirudeen Usman ya yi kira ga al’ummar Nijeriya, su zabarwa shugaban kasa Muhammad Buhari ‘yan majalisun tarayya, kwararru masu kishi da zasu taimaka masa wajen aikawar da manufofinsa sake gina kasar nan, a zaben shekara ta 2019. Dokta Nasirudeen Usman da ya fito takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya, a mazabar Lere dake jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC ya yi wannan kiran ne, a lokacin da yake jawabi ga al’ummar mazabar ta Lere, a lokacin da ya ziyarci mazabun yankin, a makon da ya gabata. Ya ce kowa ya yarda cewa shugaba Buhari yana da kyakyawar manufofi ga al’ummar kasar nan, amma a tsarin mulkin damakoradiya na kasar nan da muke bi. Ba zai iya cimma wadannan manufofi nasa ba, sai tare da goyan bayan ‘yan majalisar tarayya. Ya ce kuskure ne idan aka sake zabar shugaba Buhari amma ba zabar masa nagartattun ‘yan majalisar wakilai masu kishi irin nasa ba, da zasu je su taimaka masa. ‘’Buhari ya faro ayyuka masu yawa musamman a arewa, kamar aikin yashe kogin Neja domin jiragen ruwa su rika kawo kaya arewa daga turai, da aikin shinfida hanyar jirgin kasa ga yunkurin farfado da masana’antun da aka rufe a shiyar Kaduna da Kano. Ga aikin sake farfado da Kamfanin mulmula karafa na Ajakuta wanda aka yi kamar shekaru 40 ana magana. Ga aikin madatsar ruwa ta Mambila dake jihar Taraba. Duk matsalolin da Buhari yake fuskanta wajen gudanar da wadannan ayyuka ‘yan majalisun nan na tarayya ne, suke dakile su. Don haka mu taru mu zabo ‘yan majalisa masu kishi wadanda zasu taimakawa Buhari ya aiwatar da wadannan ayyuka, da ya faro a zaben shekara ta 2019.’’ Dokta Nasirudeen ya yi bayanin cewa babu shakka akwai bukatar a tashi tsaye wajen wayar da kan mutanen kasar nan, kan siyasa. Ya ce siyasa wata hanya ce ta cigaban jama’a. Don haka ya kamata duk wanda jama’a zasu zaba a matsayin wakilinsu, su tabbatar cewa mai kishinsu ne kuma mai gogewa ne, ba wanda zai kawo ‘yan kudi ya basu ba, bayan sun zabe shi ya kasa yin wakilcin da suka tura shi.

0
728
Dokta Nasirudeen Usman.

Isah Ahmed, Jos

MATAIMAKIN Darakta Janar na makarantar  horar da lauyoyi ta Nijeriya da ke Kano, kuma malami a makarantar koyar  da dabarun mulki da ke Kuru  a  Jos,   Dokta Nasirudeen Usman ya yi kira ga al’ummar Nijeriya, su zabarwa shugaban kasa Muhammad Buhari ‘yan majalisun tarayya, kwararru masu kishi da zasu taimaka masa wajen aikawar da manufofinsa sake gina kasar nan, a zaben shekara ta 2019. Dokta Nasirudeen Usman da ya fito takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya, a mazabar Lere dake jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC  ya yi wannan kiran ne, a lokacin da yake jawabi ga al’ummar mazabar ta Lere, a lokacin da ya ziyarci mazabun yankin, a makon da ya gabata.

Ya ce kowa ya yarda cewa shugaba Buhari yana da kyakyawar manufofi  ga al’ummar kasar nan, amma a tsarin mulkin damakoradiya na kasar nan da muke bi.  Ba zai iya cimma wadannan manufofi nasa ba, sai tare da goyan bayan ‘yan majalisar tarayya.

Ya ce kuskure ne   idan aka  sake zabar shugaba Buhari amma ba zabar  masa nagartattun ‘yan majalisar wakilai masu kishi irin nasa ba, da zasu je su taimaka masa.

‘’Buhari ya faro ayyuka masu yawa musamman a arewa, kamar aikin yashe kogin Neja domin jiragen ruwa su rika kawo kaya arewa  daga turai,  da aikin shinfida hanyar jirgin kasa ga yunkurin farfado da masana’antun da aka rufe  a shiyar Kaduna da Kano. Ga aikin sake farfado da Kamfanin mulmula  karafa na Ajakuta wanda aka yi kamar shekaru 40 ana magana. Ga aikin madatsar ruwa ta Mambila dake jihar Taraba. Duk matsalolin da Buhari yake fuskanta wajen gudanar da wadannan ayyuka ‘yan majalisun nan na tarayya ne,  suke dakile su. Don haka mu taru mu zabo ‘yan majalisa masu kishi wadanda zasu taimakawa Buhari ya aiwatar da wadannan ayyuka, da ya faro a zaben shekara ta 2019.’’

Dokta Nasirudeen ya yi bayanin cewa babu shakka akwai bukatar a tashi tsaye wajen wayar da kan mutanen kasar nan, kan siyasa. Ya ce siyasa wata hanya ce ta cigaban jama’a. Don haka   ya kamata duk wanda jama’a zasu zaba a matsayin wakilinsu, su tabbatar cewa mai kishinsu ne kuma mai gogewa ne, ba wanda zai kawo ‘yan kudi ya basu ba, bayan sun zabe shi ya kasa yin wakilcin da suka tura shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here