Amarya Ta Kashe Jaririn Kishiyarta Da Tafasasshiyar Miyar Kubewa

0
561
Rabo Haladu Daga Kaduna
RUNDUNAR \’yan sandan jihar Jigawa ta ce tana tsare da wata amarya wadda ta watsa wa uwargidanta tare da danta dan wata 10 tafasasshiyar miyar kubewa a jikinsu.
Mai magana da yawun \’yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne a garin Gantsa da ke karamar hukumar Buji ta jihar. Sai dai ya ce jajririn ya mutu sanadiyyar abin da ya faru.
SP Jinjiri, ya ce akwai rashin jituwa a tsakanin kishiyoyin.
Amaryar wadda ba ta wuce shekara 20 da haihuwa ba tana dakin girki ne a lokacin da
uwargidan, rungume da danta, ta shiga dakin dafa abincin, daga nan, sai amaryar ta fara
mayar mata da magana.
Daga nan sai cacar baki ta kaure. Ba tare da bata lokaci ba ne kuma amaryar ta dauki tukunyar miya tana tafarfasa ta watsa wa uwargidan da danta a jikinsu.
Bayan ta watsa musu miyar ne amaryar kuma ta fara ihu tana neman a kawo musu dauki.
Mai magana da yawun yan sandan ya ce uwargidan tana babban asibitin Dutse tana
karbar magani, kuma duk jikinta ya daye, amma yaron ya rasu.
Kwamshinan \’yan sandan jihar Bala ya bayar da umarnin a kai amaryar da ta aikata lamarin sashen binciken kwakwaf domin gudanar da bincike da kuma yi mata hukuncin da ya dace.
Wakilinmu ya yi kokokarin jin ta bakin mijin matan wato Malam Hamza, amma wayarsa a rufe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here