Duk Wanda Ya Sace Kudin Talakawa Fir\’auna Yake Komawa- Almustapha

0
957
Marigayi Janaral Sani Abacha
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
TSOHON Dogarin tsohon shugaban kasa Marigayi janar Sani Abacha, Manjo Hamza AL- Mustapha mai ritaya ya bayyana cewa duk wanda ya sace dukiyar kasa ya bar Talakawa cikin wahala yakan koma wani Fir\’auna ne kawai.
Hamza AL- Mustapha ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Hamza AL- Mustapha ya bayyana cewa Babu wani abin burgewa daga wajen dukkan mutumin da ya sace dukiyar jama\’a
Ya ci gaba da cewa a batun tsaron kasa ba wani sassauci da za a yi wa wani ko gungun wadansu mutane, domin sai da zaman lafiya za a iya gudanar da komai na ci gaban rayuwa.
Ya dace a fahimci cewa wuraren tsare motocin da aka rusa a Nijeriya tamkar an wulakanta tsaron kasa ne, domin a wuraren Tolget Tolget ne ake samun tsare miyagun da suke safarar makamai kuma koda mutum ya shigo da wadansu Bama Bamai za a iya samun damar tsare su domin akwai na\’urorin tsaro sosai a wadannan wurare don haka rusa su tamkar rusa tsaron kasa ne
Ya dace a tashi tsaye ta yadda za a samu sahihan bayanan wuraren da ake Kai makaman da ake shigowa da su ta tashi shin ruwan kasar nan
\”Lokaci zai yi da za mu bayyana komai Ina makudan kudin da wadansu mutane suka wuce da su? da a yanzu zaka Gamsu suna rike carbi da ajiye gashi a fuskokinsu? Ni Ina da hujjoji kuma suna nan za a kuma gabatar da su a nan gaba domin a dawo wa kasa da hakkinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here