Makarantar Kiwon Lafiya Ta Sabon Garin Rigasa Na Kara Daukaka

0
673
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
A kokarin ganin an samar da sahihan ingantattun masana harkokin kula da lafiyar jama\’a a cikin al\’umma yasa aka bude  makarantar koyar da matasa maza da mata ayyukan kiwon lafiya a Rigasa wato ( Community College Of Health) a Sabon Garin Rigasa da ke karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna tarayyar Nijeriya.
A bisa wannan dalili ne hukumar gudanarwar makarantar karkashin jagorancin Daraktan Makarantar Ibrahim Muhammad, suka kai ziyara hedikwatar kungiyar tuntuba ta arewa a ofishinsu da ke Kaduna.
Alhaji Ibrahim Muhammad ya bayyana wa shugabannin kungiyar tuntubar cewa sun Kai masu wannan ziyara ne tare da dalibansu  domin gaya masu irin ayyukan makarantar da kuma fayyace masu matsalolin da suke fuskanta da nufin samar masu da mafita.
Wannan makaranta dai mun kafa ta ne domin koyawa marayu da marasa dalihu Maza da mata da ke cikin al\’umma irin yadda ake aiwatar da harkokin lafiya da nufin samun bunkasar jama\’ar kasa baki daya.
Don haka ne yasa makarantar ke da kyakkyawar dangantaka da makarantar koyar da kiwon lafiya da ke kofar kibo cikin birnin zariya.
Hakika muna fama da dimbin matsalolin tafiyar da makarantar kamar haka ( rashin motocin gudanar da ayyuka, biyan kudin hayar wurin da makarantar ke gudanar da ayyukan ta domin a kowace shekara sai mun kashe makudan kudi akalla naira dubu dari biyu da hamsin wajen biyan haya\”.
Ibrahim Muhammad ya kara da cewa a makarantar a halin yanzu akwai Dalibai daga Jihohin Nijeriya da dama da suka hadar da Legas,kano,kaduna,katsina,Abuja da sauran jihohi kuma kusan duk kansu marasa galihu ne ko kuma marayu ma baki daya, duk da haka mun dauki nauyin karantar da su baki daya, a kokarinmu tare da Hakimin sabon Garin Rigasa Mohammad Jibril na bayar da irin tamu gudunmawar a cikin al\’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here