Kyakkyawar Alaka Ce Tsakanin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Da Ma\’aikatan Sakkwato

0
534
Mulkin Gwamna Aminu Tambuwal na tallafa wa rayukan al\'umma baki daya

Wakilinmu

DUBBAN jama\’a ne suka yi ta tofa albarkacin bakunansu dangane da yadda mulkin Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya shafe su kai tsaye a yayin gudanar da bukukuwan babbar sallar bana

Mutanen da wakilinmu ya sami zantawa da su sun gaya masa cewa Gwamnan ba ya barin ma\’aikatan gwamnatin jiharsa cikin halin kaka-ni-ka yi domin yana ba su albashinsu da hakkokinsu a kana kari, sannan suna da damar neman basussuka kamar yadda aka yi ta yi cikin shekaru 3 suka wuce. Ma\’aikaci zai dauki bashi a cire masa a hankali, idan wata bukatar ta taso masa kuma ba za a hana masa karin wani bashin ba.

Wannan kyakkyawar alaka ce ta sanya arzikin kasar Sakkwato yake bunkasa tare da hada-hadar kasuwanci a kullum. Ko shakka babu Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yana kyautata wa rayukan al\’ummomin jihar Sakkwato baki dayansu da ma na Najeriya kwata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here