An Kama Jirgin Ruwa Dauke Da Sundukai Sha Hudu Na Makamai

0
631
I G Na \'Yan Sandan Najeriya
Mustapha Imrana Abdullahi 

JAMI\’AN tsaron Afrika tan kudu sun kama wani Jirgin Ruwa dauke da sundukan makamai guda goma sha hudu.

Jami\’an \’yan sandan kasar Afrika ta kudu sun bayyana a ranar Alhamis cewa sun kama Jirgin Ruwan daukar kaya  da ke dauke da rajistar kasar Rasha da ake zargin yana dauke da haramtattun makamai da abubuwan fashewa da nufin zuwa Legas, ta tarayyar Nijeriya.

Jirgin mai suna Lada, an ruwaito cewa ya baro garin Madagaskar ne Wanda aka dakatar da shi a tashar Jiragen ruwa na Nggura da ke wajen gaba shin birnin Elizabeth, inda aka tsare su a wurin binciken jami\’an tsaro a ranar Lahadi
\” Mun fahimci cewa jirgin na dauke da miyagun abubuwan fashewa da miyagun makamai\”. Inji ta bakin mai magana da yawun tashar jirgin ruwan mai suna Olwethu Mdabula, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Amma yaki ci gaba da yunkarin bayani.

Birgediga Hangwani Mulaudzi, mai magana da yawun \’yan sandan bincike ya tabbatar wa kafar dillancin labarai ta AFP cewa Jirgin Ruwan na daukar kaya na dauke da makamai.

\” Wannan wani al\’amari ne mai matukar muhimmanci da ke bukatar kulawar gaggawa\”, inji shi.

Wata kafar yada labarai ta kasar Afrika ta kudu ta ce \’yan sanda tuni sun gudanar da bincike game da jirgin ruwan bayan wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta tsegunta masu labarin cewa akwai makamai da abubuwan fashewa na akalla Dala miliyan 3.5 a cikin sundukai wato kwantenoni 20.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here