Jawabin Sarkin Kano A Yayin Bukukuwan Sallah A Birnin Kano

0
525
Rabo Haladu  Daga Kaduna
MILIYOYIN al’umar musulmi ne suka yi sallah a masallatan Idi daban daban a
birnin da kewayen jihar Kano.
Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi, na biyu ya nanata muhimmancin kaunar juna
tsakanin musulmi. Mata da maza da yara kanana ne su ka yi dandazo a masallatan Idi daban daban fiye da dari a sassan birnin Kano da kewaye.
A jawabinsa na Sallah, mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu
Sanusi Na biyu, ya ja hankalin al’umma a kan muhimmancin zumunci da
kaunar juna, kana ya bukaci al’umma su yi katin zabe da kuma mallakar katin
zama dan kasa.
Dokta Muhammad Sani Ayagi, limamamin da ya jagoranci sallar Idi a fillin Idi na
harabar tsohuwar Jami’ar Bayero a Kano a cikin hudubar da ya gabatar kafin fara sallar idin ya tabo tarihin sallar layya kwana daya bayan tsayuwar Arfa.
Ya tabo batun hadin kai tsakanin musulmi inda ya ce hadin kai shi ne batun da ya mamaye hudubar galibin limaman da suka gabatar da huduba a yau, shi-ma Dokta Muhammad Sani Ayagi, ya yi tsokaci game da haka, ya ja hankalin ‘yan siyasa game da zabuka
masu zuwa.
A sakon sa na Salla, Gwamman Kano ya nanata aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da wanzar da zaman lafiya domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar Jama’ar Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here