\’Yar Gudun Hijra Ta Haifi \’Yan Hudu A Zamfara

0
646
Rabo Haladu Daga Kaduna
WATA \’yar gudun hijra Zainab Salisu mai kimanin shekara 33 da haihuwa, ta haifi \’yan hudu a sansanin \’yan gudun hijra na Maradun da ke jihar Zamfara.
Zainab, ta haifi maza biyu mata biyu a ranar Lahadin da ta gabata ba tare da
wata matsala ba.
Mai jegon ta je sansanin \’yan gudun hijrar ne daga kauyen Gidan Dan-Guntu da ke gundumar Maradun.
Mahaifin jariran Malam Salisu Muhammad, ya shaida wa manema labarai cewa sau daya tal
matar tasa ta je asibiti domin awo. Ya ce duk da ya ke ba ta samu wata matsala ba a yayin da ta ke dauke da cikin, ya so ta rinka zuwa awo akai- akai, amma kuma saboda
fargabar hare-haren da mahara ke kai wa ba je ba in banda sau daya.
Malam Salisu, ya ce duk da lafiyar ta lau ba ta fuskantar wata matsala a yayin da ta ke dauke da juna biyun, sun lura cewa girman cikin ya yi yawa, amma kuma da ya ke ba haihuwar fari bace, sai ba su damu sosai ba, saboda ta taba haifar \’yan biyu ma.
Mahaifin jariran, ya ci gaba da cewa da haihuwar ta zo sam bata jima tana nakuda ba, kuma ta samu taimakon ungozumomi ne a sansanin a yayin haihuwar.
Ya ce, ko da ta haifi jariran \’yan hudu, sai jami\’an da ke kula da sansanin suka dauki matar
da jariran zuwa asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau babban birnin jihar ta
Zamfara domin za ta fi samun kulawa sosai.
Rahotanni sun ce Zainab da mijinta na daga cikin \’yan gudun hijra fiye da dubu 12 da suka bar muhallansu saboda hare-haren da ake yawan kai wa a wasu yankunan jihar da suka hada da Maru da Maradun da Zurmi da Shinkafi da kuma Anka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here