A Zariya An Dakatar Da Hawan Matasa \”Dokin kara\”

0
638
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
KARAMAR hukumar Zariya karkashin jagorancin Injiniya Aliyu Idris Ibrahim da aka fi Sani da magani sai da Gwani ta bayyana cewa sun soke hawan sallah na matasa da ake kira Dokin kara\” sai abin da hali ya yi.
Biyo bayan taron kula da harkokin tsaron da karamar hukumar ta yi ne aka dauki wannan matakin.

Da yake ganawa da manema labarai Jim kadan bayan fitowa daga taron mai ba shugaban shawara a kan harkokin Kafafen yada labarai da sadarwa Alhaji Abubakar Rilwan ya ce daya daga cikin ayyukan karamar hukumar shi ne tsare dukiya da lafiyar jama\’a domin tabbatar da ingantaccen tsaro.
\”Don haka ba za a bari a samu taka Doka da Oda ba domin son zuciyar wadansu ko wani shi kadai koma waye, musamman mun samu rahotannin tsaro a karkashin kasa irin yadda iyaye ke ba yayansu makamai domin su halarci taron hawan matasa da ake kira da \”Dokin kara\”.
Kwamitin harkokin tsaron ya shawarci iyayensu da su kula da yayansu musamman ta hanyar yi masu Gargadi su kuma kiyaye halartar batun dokin kara da aka shirya yi ranar Lahadi nan domin jami\’an tsaro za su yi maganin duk wani ko wasu masu kunnen kashi da suka ki Jin magana.
Da yake today albarkatun bakinsa shaikh Ahmadu Makari Sa\’idu cewa ya yi iyaye ne jefa alhakin tarbiyyantar da yayansu a kan dukkan al\’amuran na rayuwa domin su tashi da dabi\’ar ta Gari.
Ya Kuma ce shi a matsayinsa na malamin addini yana Goyon bayan wannan mataki na dakatar da hawan matasa da aka fi Sani da \”Dokin kara\”.
Shima Sarkin Yaran Zazzau Alhaji Ibrahim Magani cewa ya yi hakika daukar matakin tun nesa da kofa Abu ne mai kyau da kwamitin kula da harkokin tsaron karamar hukumar ya yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here