An Yiwa Mata 79, Maza 16 Fyade Cikin Watanni 7 A Kaduna

0
792
 Daga Usman Nasidi
KUNGIYAR SARC da ke jihar Kaduna tayi tsokaci akan yawaitan lalata yara da ake yi inda an shigar da kararraki da ya shafi yiwa mata fyade har 95 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli 2018 – Hadda maza a wadanda aka lalata
Kungiyar ta ja hankalin iyaye a su zuba idanu sosai akan yaransu Kungiyar kula da wadanda aka yi wa fyade (SARC) da ke jihar Kaduna ta bayyana cewa an shigar da kararraki da ya shafi yiwa mata fyade har 95 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli 2018.
Wata jigo kungiyar Juliana Joseph ta sanar da hakan a hira da tayi da manema abarai a ranar Litinin, 27 ga watan Agusta a Abuja .
Ta kara da cewa bisa ga kararrakin da suka saurara a tsakanin wannan lokaci 16 daga cikin wadanda aka lalata maza ne.
Uwargida Joseph ta ce bisa ga bayanan da suka samu daga wajen wadanda aka yi wa fyaden sun nuna cewa 19 daga cikinsu makwabta ne suka aikata masu hakan, bakwai kuma masu gadin gidajen su, 10 kuma daga ‘yan uwa ne suka lalata su.
 “Wuraren da aka fi aikata wannan ta’asa a Kaduna sun hada da Tudun Wada, Kakuri Kudenden, Nasarawa, Hayin Banki, Gonin Gora, Dan Bushia, Romi da Rigasa.”
A karshe ta yi kira ga iyaye da su sa rika sanya idau kan ‘ya’yan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here