Ranar Da Kwankwaso Ya Bar APC Ban Yi Bacci Ba Don Murna – Ganduje 

  0
  520
  Gwamna Abdullahi Ganduje
  Daga Usman Nasidi
  GWAMNA Ganduje yayi wa tsohon ubangidan sa Kwankwaso kaca-kaca – Yace ranar da Kwankwaso ya bar APC bai yi bacci ba.
  Yace Kwankwaso tamkar Kansa ce a gare shi Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kwatanta tsohon gwamnan jihar kuma Sanata a majalisar dattijan Najeriya,
  Hakazalika gwamnan jihar ya bayyana cewa ranar da tsohon uban gidan nasa ya bar jam\’iyyar APC ya koma PDP bai yi bacci ba saboda murna don kuwa daman ya zamar masa kadangaren bakin tulu ne.
  Majiyarmu ta samu labarin cewa Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu jiga-jigan tafiyar sa a gidan gwamnati jihar lokacin da suka kai masa ziyarar ban girma da kuma barka da Sallah.
  Gwamnan ya kara da cewa shi Kwankwaso ya cika son kan sa don haka ne kuma ya yanke shawarar datse duk wata hulda dake a tsakanin su.
  A wani labarin kuma, mun samu cewa matasa a jihar Adamawa dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan sun yi wa Gwamnan jihar ta su Umaru Jibirilla Bindow ihu a wajen taron kaddamar da fara aikin hanyar gwamnatin tarayya a jihar.
  Matasan wadanda suka nuna rashin jin dadin su game da salon mulkin gwamnatin jihar sun yi ta yin ihu tare da nuna rashin gamsuwar su a lokacin da ake kirari daga saman mumbarin \’yan siyasar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here