An Kama Mutum 57 A Jihar Legas Bisa Zargin Luwadi

0
560

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

\’YAN sanda sun kama mutum 57 a Lagos da ake
zargin \’yan luwandi ne.

YAN sandan jihar sun ce an kama mutanen ne a wani otal yayin da suka taru wajen wani biki na shigar da su kungiyar \’yan luwadi.
Kwamishinan \’yan sandan jihar ta Lagos Edgal Imohimi ya shaida wa manema labarai cewa, an kama mutanen ne bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu.

Kakakin rundnar \’yan sandan jihar, Chike Godwin Oti, ya tabbatar wa manema labarai kama mutanen. Kuma ya ce an kama mutanen ne a lokacin da suke tsaka da shan miyagun kwayoyi da aka haramta irin su Tramadol, da tabar wiwi.
Sai dai wasu daga wadanda ake zargi sun musanta zargin. Wasunsu kuma sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN cewa rakiya kawai suka je wajen bikin, wasu kuma sun ce su \’yan rawa ne, yayin da wasu kuma suka ce abinci kawaisuka kai wa masu bikin, a lokacin da aka yi awon gaba da su.
Rundunar \’yan sandan dai ta ce da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da mutanen da ake zargi gaban kotu.

Auren jinsin guda, ko luwadi ko madigo sun haramta a dokar kasa, inda a 2014 aka tanadi daurin shekara 14 ga duk wanda aka samu da laifin.
Sai dai wasu masu rajin kare hakkin \’yancin bil\’adama na cikin gida da waje na sukar irin matakan da hukumomi ke dauka kan masu luwadi da madigo.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here