Dalilin Sauya Shekata Zuwa Jam\’iyyar Adawa Ta PDP – Ammani

  0
  547

   

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  DAN takarar majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Kawo Alhaji Ibrahim Ammani, ya bayyana cewar rashin gamsuwa da yadda APC ke gudanar da harkokin ta a Jihar Kaduna shi ne babban dalilin shi na sauya shekarsa daga jam\’iyyar APC ya koma jam\’iyyar PDP domin samun zarafin kawo sauyin da yake muradi.

  Dan siyasar ya bayyana hakan ne a gaban manema labarai lokacin da ya ziyarci sakatariyar jam\’iyyar PDP ta jihar Kaduna domin shaida yadda sayar da takardar tsayawa takara da PDP ta fara a talatar nan.
  Ibrahim Ammani ya cigaba da cewar tsarin tafiyar APC a jihar Kaduna ya gamu da kalubale sosai, sakamakon tauye hakkin \’ya\’yan jam\’iyyar da akeyi inda ba a bada dama \’ya\’yan jam\’iyyar na zaban wakilai da kansu sai ana musu dauki dora, inda ya bada misali da zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar, zaben da aka yi shi ba tare da gudanar da zaben fitar da gwani ba, lamarin da ya sanya \’ya\’yan jam\’iyyar da dama fusata da kuma daukar matakin ficewa daga jam\’iyyar zuwa easu jam\’iyyu musanman PDP.
  Dan takarar majalisar wanda gogaggen Dan jarida ne, ya koka dangane da irin wakilcin da mazabar Kawo ke samu a tsawon lokaci, inda ake tura wakilai masu zaman dumama kujera kawai, haka ya sanya yankin mazabar Kawo ya zama a baya wajen cigaban rayuwa.
  Ibrahim Ammani ya yi alkawarin kawo sauyi da sauya fasalin wakilcin mazabar Kawo a majalisar dokokin jihar Kaduna, idan Allah ya nufe shi da zama Dan majalisar dokokin jihar a shekarar 2019, sannan yayi kira ga jama \’ar mazabar kawo da jihar kaduna gaba daya da cewar su tashi gaba daya wajen ganin sun mallaki katin zabe na din din, domin shine makami a garesu wajen zaben shugabanni na kirki da kuma kawar da baragurbi.

  utum bayan mutum, domin akwai babban hatsari dangane da hakan. A cewar MS Usta

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here