Gundumar Kawo Za Ta Sayawa Dan Takara Ibrahim Ammani Fom

  0
  517

   

  Mustapha Imrana Abdullahi

  Kungiyar tuntuba ta Matasan yankin gundumar Kawo wato \”Kawo Youth Consultative Forum\” a turance, ta bayyana cewar za ta sayawa dan takarar kujerar majalisar dokokin jihar mai wakiltar yankin Ibrahim Ammani Fom na tsayawa takara, kasancewar shine Dan takara kwakkwara tilo wanda zai iya tsamar da yankin Kawo daga koma baya da yankin yake ciki tsawon lokaci sakamakon rashin wakilai nagari da yankin ya samu tsawon lokaci a majalisar dokokin jihar.

  Shugaban kungiyar cigaban Matasan gundumar Kawo Kwamared Musa Muhammad ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi a yayin wanin gagarumin taro da Kungiyar ta shirya domin karrama Ibrahim Ammani, wanda ya gudana a babbab zauren taro na gidan Arewa watow Arewa house dake garin Kaduna.

  Matasan gundumar Kawon sun cigaba da cewar, sun dauki tsawon lokaci suna nazari da binciken dukkanin \’yan takarar da suka fito neman kujerar dan majalisar yankin daga jam\’iyyu daban daban, bayan karantar kowane Dan takara da suka yi ne, daga karshe suka fidda Ibrahim Ammani a matsayin wanda za su marawa baya, sannan suka yanke shawara saya mishi Fom na takarar da bashi dukkanin goyon bayan da ya kamata domin kaiwa ga samun nasara.

  Kwamared Musa Muhammad ya kara da cewar, dukkanin abinda ake bukata na cancantar yin wakilci Ibrahim Ammani yana da su, na farko Matashi ne sannan mai ilimi ne na zamani dana addini, sannan gogaggen Dan jarida ne wanda ya jima yana bayar da tashi gudummuwa wajen ilimantarwa da wayar da kan jama\’a domin su san \’yanci da hakkin su, wanda kuma a yanzu haka shine Sakataren kudi na kungiyar \’yan jaridu ta kasa reshen jihar Kaduna, lallai duk wanda yake da wannan matsayi ya dace ya wakilci jama\’a a ko\’ina inji Matasan.

  Anata jawabin shugabar bangaren Mata ta kungiyar Sister Aisha Abdullahi, ta ce ya zama wajibi garesu da dukkanin wani mai kishin gundumar Kawo da Karamar hukumar Kaduna ta Arewa da jihar Kaduna baki daya, dasu goyi bayan Honorabul Ibrahim Ammani, domin Mutum ne wanda ya jima yana bada taimako ga jama\’a musanman marasa karfi, ya dauki nauyin karatun yara da dama har sun zama mutane, bangaren ayyukan yi kuwa Matasan gundumar Kawo da suka samu abinyi sanadin Ibrahim Ammani basu kirguwa, kuma wannan shine dalilin da ya sa mu jama\’ar Kawo muka bukace shi da ya fito domin wakiltarmu a majalisar dokokin jihar, kuma tun da Allah yasa ya amince muke godiya ga Allah domin mai share mana hawaye ya fito, kuma shine Dan majalisarmu da yardar Allah a 2019.

  Lokacin da yake maida jawabi, Honorabul Ibrahim Ammani ya godewa kungiyar Matasan gundumar Kawon bisa karrama shi da suka yi, kuma yayi alkawarin ba zai basu kunya ba akan yarda da amincewar da suka yi mishi, yace a halin yanzu a cikin jam\’iyyar su ta PDP su bakwai ne suka nuna sha\’arwarsu ta tsayawa takarar Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Kawo, kuma a halin da ake ciki yanzu tattaunawa tayi nisa a tsakanin \’yan takarar, kuma da yardar Allah za su amince su marawa mutum guda a cikin su baya domin samun nasarar jam\’iyyar, kuma cikin ikon Allah sun hango samun nasara a tafiyar, idan Allah ya yarda PDP za tayi nasara a zabukan \’yan majalisar dokokin jihar dama jihar baki.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here