Miyagun Mutane Daga Zamfara Suna Barna A Katsina

0
630

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

YAYINDA sojojin saman kasarnan ke ci gaba da fafatawa da miyagun mutane a jihar Zamfara suna rugurguza sansanoninsu, ana samun wasu suna sulalewa cikin jihar Katsina inda gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya ce suna satar mutane tare da yin fashi da makami a kananan hukumomi tara Jiragen yakin sojojin sama sun yi rugurugu da wasu sansanonin \’yan bindiga a jihar Zamfara.

Jiragen yakin sun tarwatsa \’yan bindigan dake yankunan Shinkafi, Galadi, Aja, Gaji Bawar, da sauran wasu wuraren.

Babban hafsan hafsoshin mayakan saman Nigeria Air Marshal Sadique Abubakar yace aikin \’yan bindigar tamkar yaki ne saboda haka suka yi damarar fafatawa yanzu. Yadda mutane ke daukan manyan bindigogi
su shiga gari su soma kashe mutane haka siddan, yaki ne a fahimtarsu.

Dangane da yadda abun dake faruwa a jihar Zamfara ke shafar jihar Katsinadake makwaftaka da ita, gwamnan jihar ta Katsina Alhaji Aminu Bello Masari cewa ya yi mutanen da sojoji ke fatattaka daga Zamfara, suna shigowa jiharsa suna satar mutane da yin fashi da makami.Suna garkuwa da mutane a dazuzzukan na Zamfara sai an biyasu kudin fansa sannan su sako su.

Kamar yadda gwamnan Katsina ya yi bayani kananan hukumomi tara da suka yi iyaka da dajin Zamfara lamarin ya shafa. Kananan hukumomin da lamarin yafi shafa su ne Jibiya, Batsari,

Safana, Dan Musa, Kankara da Faskari. Akwai wasu \’yan binidgar kuma a dajin Birbis wanda yake kusa da Zamfara da Faskari da kuma Sabuwa.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here