Yadda Tashar Manyan Motoci Ta Kasuwar Dawanau Ta Lalace

  0
  774

   

  JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

  KASUWAR Dawanau ta kasance wani dandali na hadahadar kayan abinci ta duniya tun kimanin shekaru talatin ko fiye, inda baki daga kasashe daban-daban na fadin duniya suke zuwa suna saye ko sayar da kayan abinci nau\’i daban-daban.

  Haka kuma ana samun kusan kowane irin kayan amfanin gona da ake dasu a sassa daban-daban musamman wadanda ake sarrafawa a kamfanoni da masana\’antu na ciki da wajen kasarnan.

  Bugu da kari, a kasuwar Dawanau ana fitar da nau\’i-naui na kayan abinci zuwa kasashen nahiyar Afirka da kuma sauran sassa na duniya, wanda hakan ce ta sanya kasuwar take rike da kambun ta rani da damina.

  Sai dai kasuwar ta Dawanau tana fama da matsaloli masu tarin yawa wadanda suka hada da rashin kyawun hanyoyin cikin kasuwa da rashin magudadun ruwa a wasu bangarorin da kuma rashin yin cikon kasa a guraren da ruwa ke kwanciya cikin kasuwar.

  Haka kuma babban abin da yafi addabar kasuwar ta Dawanau shine yadda tashar manyàn motoci take a lalace musamman idan akace ruwan damina ya sauka, wanda kuma hakan ta sanya dole sai dai idan ire-iren wadannan manyan motoci suka kai kaya kasuwar suke tsayawa bakin babban titi ana dauka kadan-kadan.

  Mafiya yawan direbobin manyan motocin da wakilin mu ya tattauna dasu sun nuna mamakin su bisa yadda wannan tasha ta motoci ta lalace musamman lokacin damina duk kuwa da irin harajin da ake kaba daga garesu batare da tsaiko ba.

  Haka kuma wasu masu sayara kayan abinci dake cikin kasuwar ta Dawanau sun bayyana cewa akwai bukatar a ingana nnan guri musamman ganin yadda daga kowace nahiya ana zuwa saye ko sayar da kayan abinci nau\’i-nau\’i.

  Bugu da kari, masu sana\’ar daukar kaya watau \’yan dako sun nunar da cewa akwai gurare maau yawa da suka lalace amma ko kadan ba\’a kula su tareda yin kira ga hukumomin da kasuwar take a hannunsu dasu yi kokarin bunkasa kasuwar.

  Wakilin kaauwar Malam Shehu Ali Oyes ya bayyanawa wakilin mu cewa tuni shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa ya ziyarci kasuwar tareda duba dukkanin guraren da suke da bukatar kulawar gaggawa domin a fara gyara da zarar ruwan sama yayi sauki.

  Sannan ya tabbatar wa da yan kasuwar ta Dawanau cewa majalisar karamar hukumar ta Dawakin Tofa zata yi ingantaccen gyara a kaauwar ta Dawanau domin kara kyautata yanayinta, inda daga karshe ya jaddada cewa zai ci gaba da wakilcin kasuwar bisa adalci da sanin ya kamata ta yadda kowa zai ji dadin harkarsa cikin ta.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here