A Karshe Shekarau Ya Koma APC

  0
  789

   

  Mustapha Imrana Abdullahi

  BAYANAN da ke fitowa daga Jihar Kano ta bakin mai magana da yawun tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim shekarau na cewa Malam Ibrahim Shekarau tare da magoya bayansa duk sun fice daga PDP zuwa APC

  Kamar dai yadda Alhaji Sule Ya\’u Sule ya shaidawa kafar labarai ta daily trust ya ce babban dalilin da yasa suka canza shekar daga PDP zuwa APC biyo bayan irin tashin adalcin da suke cewa an yi masu ne, wannan shi yasa bayan an tattake wuri lokacin da shekarau da magoya bayansa suka yi taro aka yanke hukuncin ficewar.

  Kamar yadda sule Ya\’u ya ce \”Ina son in tabbatar maku cewa Shekarau ya yanke shawarar ficewa daga PDP zuwa APC sakamakon irin rashin adalcin da aka yi Masa tare da mutanensa, kuma wannan shugabannin PDP ne suka aikata hakan\”.

  \”Ubangida na shekarau ya hadu da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a Abuja sun Kuma tattauna batun komawa APC. Zai kuma tattauna da masu ruwa da tsaki a Kano domin ayi taron Komawarsa a fili gaban jama\’a\”.

  Sule ya tabbatar da cewa babu ta yadda za su yi su ci gaba da zama cikin PDP suna kallon shugabannin PDP na kasa suna yin abin da suke so musamman sai abin da kwankwaso yake bukata duk a yi watsi da abin da manyan Yan jam\’iyya za su fadi.

  Ya ci gaba da cewa shekarau ya yi tuntuba mai zurfi inda ya tattauna da jama\’a masu yawa da suka hadar da magoya bayansa bayan an yi mahawara mai zafi a karshe an yanke shawarar a fice daga PDP zuwa APC.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here