AN NADA UWAR GIDAN GWAMNAN JIHAR KADUNA MAGAJIYAR SAMINAKA  

0
1022

Isah  Ahmed, Jos

 

Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada Uwar gidan gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hadiza El’Rufa’i  magajiyar Saminaka, a ranar litinin din da ta gabata a lokacin da ta ziyarci karamar hukumar Lere, don ganawa da matan karamar hukumar.

Da yake jawabi a wajen Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya bayyana cewa an nada uwar gidan gwamnan magajiyar Saminaka ne, domin nuna godiya ga irin dimbin ayyukan raya kasa da mai girma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El’Rufa’i ya yi a yankin, da kuma kara donkon zumunci.

Ya yabawa uwar gidan gwamnan kan wannan ziyara da ta kawo yankin. Ya bada tabbacin cewa al’ummar yankin zasu cigaba da baiwa gwamnatin jihar Kaduna da gwamtin tarayya goyan baya da hadin kai. Domin  cimma kudurorin bunkasa kasa da suka sanya a gaba.

A nata jawabin uwar gidan gwamnan na jihar Kaduna Hajiya Hadiza El’Rufa’i ta bayyana cewa sun fara wannan ziyarce ziyarce da karamar hukumar Lere ne, saboda mahimmancin da karamar take da shi.

Ta ce gwamnatin jihar Kaduna tayi ayyuka da dama musamman a bangaren raya ilmi da kiwon lafiya a wannan  karamar hukuma.

‘’Gwamnatin jihar Kaduna taso tayi ayyuka fiye da haka a  wannan yanki, amma saboda yadda ‘yan majalisar dattawa na jihar Kaduna, suka ki yarda a samo rance daga bankin duniya ya sanya ba a sami damar aiwatar da wannan kyakyawan kuduri ba’’.

Daga nan ta nuna matukar farin cikinta kan irin tarbar da aka yi mata. Ta ce a gaskiya tayi matukar farin ciki ganin yadda dimbin matan wannan karamar hukuma suka fito suka tarbi tawagarta.

Shima a nasa jawabin shugaban karamar hukumar Lere Alhaji Abubakar Buba ya bayyana cewa  babu shakka wannan ziyara da uwar gidan gwamna ta kawo  wani babban karamci ne ga karamar hukumar.

Ya bada tabbatacin cewa al’ummar karamar hukumar  zasu bayar da kuru’u  ga shugaban kasa Muhammad  Buhari da gwamnan jihar Kaduna Malam  Nasiru El’Rufa’i fiye da kowannce karamar hukuma a yankin zone 1 na jihar Kaduna a zabe mai zuwa.

‘’Karamar hukumar Lere, karamar hukuma ce mai dimbin albarka musamman kan aikin noma a Nijeriya. Domin mu nuna miki cewa mu manoma ne, matan karamar hukumar nan sun baki kyautar buhun masara da buhun shinkafa  da buhun wake   da kuma rake’’.

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here