Barayi Sun Kai Hari Gidan Shugaban Mafarautan Yankin Toro Sun Kashe Mutum Uku

0
659

 

Isah  Ahmed, Jos

 WASU mahara da ake kyautata zaton barayi ne, sun kai hari gidan shugaban kungiyar mafarauta ta Danga Security dake karamar hukumar Toro a jihar Bauchi, Alhaji Yusuf Abdullahi a gidansa dake garin Magama. A inda suka bude wuta da bindigogi suka kashe masu gadin gidan mutum uku, tare da kone gidan gabaki daya a daren ranar asabar din da ta gabata.

Da yake yiwa wakilinmu karin bayani kan wannan al’amari da ya faru, shugaban kungiyar mafarautan ta Danga Security  Alhaji Yusuf Abdullahi wanda  kuma dan kasuwa ne mai harkokin kasuwancin sayar da ma’adanan  dutse, ya bayyana cewa bayan ya fita gida yana garin Magama Gumau a ranar da wannan al’amari ya faru,  bayan sallar magari ba, sai ya  taso zai taho gida Magama.

Ya ce  sai makocinsa  ya kira shi  a waya yace masa barayi  sun shigo gidansa, har sun sanyawa gidan wuta.

Alhaji Yusuf Abdullahi ya yi bayanin cewa nan take ya  kira jami’an tsaro na Magama Gumau ya  fada masu ya kira mai Gunduma na Magama Gumau ya fada masa.

‘’Yayana yaje wajen da aka ajiye sojoji a kusa da wannan gari na Magama  ya faxa masu abin dake faruwa,  suka ce ba a basu umarni ba. Hankalina ya tashi, na tashi zan tafi wajen ‘yan sanda suka hana ni, saboda babu wani makami a hanuna. Wadannan barayi sun sanya wuta a gidan  kuma iyalaina matana 2 da ‘yayana 9 duk suna cikin’’.

Ya ce bayan da barayin suka tafi, da suka zo suka tarar sun kone gidan gabaki daya kuma  sun kashe masu gadin mutum uku. Wadanda suka hada da Umar Fareti  da Auwalu Muhammad da kuma Jamilu.

Ya ce wadannan masu gadin  suna zama a wannan gidan ne suna gadinsa da suka zo suka same su a wajen gidan, suka  bude masu wuta da bindigogi suka kashe su.

Ya ce kafin wadannan barayi su kona gidan sun shiga cikin gidan suka yi ta harbe harbe da bindigo  a cikin gidan, amma Allah ya tsarar  da iyalansa  gabaki daya babu wanda ya rasa ransa.

Ya  ce barayin sun shedawa   amaryarsa cewa  ta fada masa   sata yanzu suka fara. Kuma ta fada masa ya bar aikin nan da yake yi,  idan ya bar aikin nan ya rabu da su, shi  ke nan. Idan kuma bai bar aiki nan ba, yana nan tare dasu. Domin ya takura masu.

Ya ce ganin yanayin abubuwan da suke faruwa a wannan karamar hukuma na yadda barayi suke damunsu da ta’addanci da fashi da makami,  yasa ya shiga wannan aiki.

‘’Babu shakka na takuwa barayi a wannan yanki na Toro ta hanyar wannan kungiya da nake yiwa jagoranci ta Danga Security, domin  na sha kama barayi da bindigogi ina kaiwa jami’an tsaro,  amma su dawo. Wasu ma basa fin mako biyu, sai a sako su. Wadannan mutane suna ta fadin cewa zasu kashe ni. Na sha yin rubutu ina kaiwa jami’an tsaro kan wannan al’amari. Ina rokon a daina sako irin wadannan mutane da nake kamawa’’.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan  jihar Bauchi DSP Kamal Datti kan faruwar wannan al’amari,   ya tabbatar cewa wannan al’amari ya faru.

Ya ce sun je gidan wannan mutum tare da kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, don ganin abin da ya faru. Ya ce   suna ganin kamar wadannan mahara sun zo ne don su hallaka wannan mutum,  domin basu dauki komai ba a gidan. Amma  sun kashe masu gadin gidan mutum uku, kuma sun kona gidan gabaki daya.

DSP Kamal ya yi bayanin cewa rundunar ‘yan sandan ta jihar Bauchi tana nan tana bincike,  don gano wadannan mutane da suka aikata wannan al’amari, don gurfanar da su a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here