TSARIN DA APC TA KAWO NA ZABEN ‘YAN TAKARA YA YI DAIDAI-DOKTA NASIRDEEN  

  0
  476

  Isah Ahmed, Jos

   

  WANI dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya na mazabar karamar hukumar Lere da ke jihar Kaduna karqashin jam’iyyar APC,  kuma Mataimakin darakta Janar na makarantar horar da lauyoyi ta Nijeriya da ke Kano, Dokta Nasirudeen Usman ya bayyana cewa tsarin da uwar jam’iyyar APC ta kasa ta kawo, na yadda za a gudanar da zaben tsayar da  ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben da za a gudanar a badi, ya yi daidai. Dokta Nasirudeen Usman ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Ya ce tsarin da jam’iyyar APC ta kawo na zaben ‘yan takara ya yi daidai. Wato a zaben shugaban kasa ayi tsarin zaben yar tinke,  a tsarin zaben gwamnoni da ‘yan majalisu na tarayya da jihohi abi tsarin zaben wakilan jam’iyya.

  Ya ce abin da yasa uwar jam’iyya ta ce abi tsarin zaben wakilan jam’iyya a jihohi, ta lura da wasu matsaloli da zasu iya tasowa a wasu jihohi, idan ba irin wannan zabe aka yi ba. Don haka aka baiwa kowace jiha zavi, taje ta zabi tsarin zaben da take so, wanda ba zai kawo wata matsala ba.

  Dokta Nasirudeen Usman ya yi bayanin cewa tun da aka dawo mulkin damakoradiya, jam’iyyar APC ce kawai ta baiwa ‘yayanta  irin wannan dama. Ya ce babu shakka  wannan mataki da jam’iyyar APC ta xauka zai karfafa mulkin damakoradiya a Nijeriya.

  Dokta Nasirudeen ya ce ko mutum 100 ne zasu fito su yi takara da shugaban kasa Muhammad Buhari, kan kujerar shugabancin kasar nan, ba zasu sami nasara ba. Domin ‘yan Nijeriya sun ga irin kokarin da shugaba Buhari yake yi wajen farfado da kasar nan. Don haka ba zasu bar wannan dama da suka samu ba.

  Ya ce idan shugaba Buhari ya cigaba da mulki nan da shekara 4 masu zuwa zai dora kasar nan kan kyakyawan turba tagari.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here