Sani Sidi Ya Kai Ziyara Birnin Gwari

  0
  700

  Mai neman kujerar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Sani Sidi OFR, ya kammala ziyarar da yake kaiwa kananan hukumomin Jihar domin ganawa da yayan PDP.

  Duk da irin matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin Birnin Gwari amma Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Sani Sidi tare da dimbin magoya bayansa sun Kai ziyarar ganawa da magoya bayan Jam’iyyar PDP da ke karamar hukumar Birnin Gwari.

  Alhaji Sani Sidi Wanda ya kasance tsohon shugaban hukumar bayar da Agajin Gaggawa ne ta kasa wato (NEMA) a ranar Larabar nan ne ya Kai ziyarar tuntuba inda ya gana da shugabannin PDP da kuma masu ruwa da tsaki tare da deliget da za su yi zaben fitar da dan takara a karkashin PDP.

  Da yake ganawa da yayan jam’iyyar magoya baya a lokacin ziyarar tuntubar a garin Birnin Gwari Sani Sidi ya shaidawa jama’ar cewa ya zo ne tare da jirgin yakin neman zabensa domin jajantawa game da irin dimbin rayukan da suke salwanta a wannan yankin.

  “Mun zo ne domin jajanta wa musamman ganin irin radadin zafin da kuke ciki na salwantar rayuka da ya Dade yana addabar wannan yanki, a gaskiya Ina damuwa matukar gaske da halin da kuke ciki”, Sidi ya bayyana a cikin sanyin murya da tattausan lafazi

  Kamar yadda Sani Sidi ya bayyanawa jama’ar cewa an yi ta bani shawara a kan zuwana Birnin Gwari saboda irin matsalar tsaron da ake fama da ita. An bani shawarar cewa in gayyace Ku Kaduna domin mu tattauna da ku, amma naki amincewa da irin wannan shawara don haka na yanke shawarar zuwa da kaina tare da Tawagar neman zabe na baki daya mu iske Ku har gida a wannan mawuyacin lokaci.

  “A matsayina na mutum hakika Ina samun bacin rai a duk lokacin da na tuna abin da ke faruwa a a wannan wuri don haka Naga ta yaya zan zauna a Kaduna in gayyace Ku ta yaya mutum zai nemi Alfarma ga mutanen da ba zai iya ziyarta ba?

  Don haka muka yanke shawarar zuwa nan domin tabbatar maku cewa lamarin wannan yaki na kan gaba cikin kalubalen da zamu tunkara idan Allah ya bamu ikon kafa Gwamnati domin yi maku jagoranci” inji Sidi.

  A jawabansu daban daban Yan siyasa da shugabannin al’umma duk sun yi wa Sani Sidi alkawarin bashi Goyon baya a lokacin zaben fitar da dan takara a jam’iyyar PDP.

  Kamar yadda shugaban masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar Alhaji Abdulkadir Jibril Waziri Birnin Gwari cewa ya yi zuwan Sani Sidi wannan wuri alamace ta shi kadai ne Dan takarar da ya ziyarci Birnin Gwari.

  ” Hakika ziyarar tasa ta bayyana karara a fili cewa ya samu da irin halin da muke ciki domin Babu wani Dan takarar da ya gayyace mu. Wasu kadan daga cikin su ne suka gayyace mu zuwa Kaduna domin suna Jin tsoro saboda haka muke ganin ta yaya mutum zai jagoranci wadanda bai San matsalarsu ba? A saboda haka ne muka yanke shawara baki daya cewa zamu bashi kuri’armu baki daya idan lokacin zaben fitar da dan takara yazo ” inji Waziri.

  Mutumin da yake kan gaba a rukunin Yan takarar da suke neman kujerar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin PDP Alhaji Sani Sidi ya kai ziyarar tuntuba domin ganawa da yayan jam’iyyar da kuma masu zabe domin neman kuri’arsu a ranar zaben da ake son yi a ranar 26 ga watan Satumba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here