2019: Buhari Ya Gaza Amma Babu Wani Da Zai Iya Rikon Najeriya Da Gaskiya Cikin Sauran Yan Takara – Balarabe Musa

0
597

 

Daga Usman Nasidi

GABANNIN zaben 2019, tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jigon kungiyar dattawan arewa, Balarabe Musa ya yi duba sosai ga harkokin kasar sannan ya bayyana cewa koda dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gazawa ýan Najeriya tun bayan zabarsa a 2015, babu dan takara ko daya daga jam’iyyun adawa da ya shirya kai Najeriya inda take mafarkin kaiwa.

Tsohon gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba yace tulin yan takaran dake neman shugabanci a yanzu babu wadda ya nuna cewa zai sanya ci gaba al’umma sama da son zuciyarsa.

A cewarsa, kasar na bukatar ingantaccen shugaba a 2019 wadda zai hada kan kabilun kasar, yayi amfani da samunta wajen yiwa mutane aiki sannan ya kawo karshen cin hanci da rashawa a manyan wurare.

Ya kuma koka akan tsarin shiga lamarin siyasa a kasar, cewa tsadar abun shi ya hana wadanda ke son kawo ci gaba fitowa tsanin siyasar kasar.

Hakazalika idan ba a manta ba a jawabin shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki ya yi a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba ya bukaci ýan Najeriya da kada su nuna kabilanci wajen zabar shugabanni kawai abunda zasu duba shi ne hangen nesan shugaba wajen kawo chanji.

Saraki dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan a Lagas yayinda yake jawabi ga mambobin jam’iyyar. Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa ziyarar da ya kai sakatarioyar jam’iyyar na daga cikin rangajin da yake na neman goyon baya akan kudirinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here