Gwamnatin Katsina Za Ta Fara Aikin Mayar Da Dalibai

0
654
Gwamna Aminu Bello Masari

 

Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNATIN Jihar Katsina karkashin Jagorancin Alhaji Aminu Bello Masari na sanar da jama\’a cewa tuni aka kammala shirye shiryen Fara daukar Dalibai da suke karatu a makarantun sakandare na hada ka domin mayar da su makarantun da suke karatu na sakandare a daukacin Jihohin arewacin Nijeriya 19, ga dai yadda tsarin zai kasance.

A ranar Litinin 24 ga watan Satumba 2018 masu karatu a Jihohin Bauchi, Taraba,Kebbi,Sakkwato,Filato,Nasarawa,Gombe da Jihar Adamawa duk za a dauke su domin mayar da su makarantun da suke karatu a wadannan jihohin da aka lissafa

Sai ranar Alhamis 27 ga watan Satumba 2018 Jihohin Kaduna,kwara,Neja,Kano,Jigawa da Yobe, kuma ana sanar da jama\’a cewa batun daukar yaran zuwa makarantun ya hada da Sababbin Dalibai.

Sai dai masu karatu a Jihohin Banuwai da Zamfara za a sanar da lokacin su nan gaba.

Wannan sanarwa na dauke da sa hannun jami\’in yada labarai na ma aikatar ilimin Jihar katsina Salisu Lawal Kwaru  a madadin kwamishinan ma aikatar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here