Mata Manoma Suna Bukatar Tallafi Na Musamman-Inji Hajiya Sidiya AFAN

0
813

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAR bangaren mata ta kungiyar manoman Nijeriya reshen jihar kano watau AFAN, Hajiya Sidiya Fatima Sherif Gambo Yako tace mata manoma dake kasar nan suna bukatar tallafi na musamman daga gwamnati ta yadda zasu bunkasa noman da suke yi cikin nasara.

Tayi wannan bayani ne cikin tattaunawar da suka yi da wakilin mu, inda ta nunar da cewa matan kasar nan tuni suka amsa kiran gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci wanda hakan ya taimaka matuka wajen farfado da arzikin kasa da samar da aiyukan yi kamar yadda abin yake a yanzu.

Sannan ta sanar da cewa ko shakka babu manufofin shugaban kasa Muhammasu Buhari kan sha\’anin aikin gina suna dakyau musamman ganin yadda Nijeriya ta kama hanyar dogaro dakai ta fuskar noma, tareda yin kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi dasu kara bullo da kyawawan tsare-tsare na taimakawa mata manoma domin su bunkasa noman da suke yi rani da damina.

Hajiya Sidiya Fatima Sharif Gambo Yako tayi amfani da wannan dama wajen bayyana irin yunkurin da kungiyar su keyi domin tallafawa mata manoma, wanda a cewar ta shirye-shirye sunyi nisa wajen yin jogoranci ga mata manoma domin su amfana daga wannan shiri na tallafawa manoma mata.

Daga nan sai ta yabawa shugaban kasa Muhmadu Buhari fa gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da kuma su kansu cibiyoyin kudi da suka hada hannu da wasu kungiyoyi wajen ganin manoman wannan kasa suna samun tallafin noma batare da tsaiko ba, tareda jaddada cewa zasu taimaki mata manoma kamar yadda suka tsara.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here