Mun Daura Dammarar Kawar Da Muhamman Usman – Eja Gubuci

  0
  664
  Gwamna Malam Nasir El-Ruffa\'i na Jihar Kaduna

   

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  TSOHON kantoman rikon karamar hukumar Makarfi a Jihar Kaduna Alhaji Salisu Eja Gubuci, ya bayyana cewa su a matsayinsu na cikakkun yayan jam\’iyyar APC ba za su amince da ayi masu cushen wani Dan takara ba a Kowane irin mataki.

  Salisu Eja Gubuci ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.

  Eja Gubuci ya ce hakika su a matsayinsu na Yan asalin karamar hukumar Makarfi sun shirya tsaf domin Fara yakin dawo wa da dan majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Makarfi da Kudan Honarabul Muhamman Usman.

  Kamar yadda ya ce hakika wakilcin Muhamman Usman dai bai amfana wa jama\’ar komai ba don haka ba gudu ba ja da baya wajen yakin dawo da shi gida ta yadda za su Zabi ingantaccen sahihin wakilin da zai kula da mutanen Makarfi Da Kudan.

  \”Ba zamu amince ayi mana cushen wani Dan takara ba, a Kowane irin mataki\”

  Ya ci gaba da cewa \”Ta yaya za su rika yin biyayya da rungumar mutumin da yana wakiltar jama\’a amma ba zai iya shiga cikin al\’umma ba? Don haka ba zamu bi mutumin da idan an Je yawon kamfe za a taka mu da gudu muna buya cikin duhun dawa ko a cikin duhun rake ba kasancewar ana maganar karkara ne\”. Inji Eja Gubuci.

  Ya dai fayyace cewa hakika ya dace a Sani cewa Dan PDP ba zai tuba ba don haka Gwamnatin APC kada ta sake ta cusa masu Dan takarar da ya kasance Dan PDP kuma Wanda ba Dan karkara ba

  \”Domin kasancewar mu mutanen karkara hakika sanatan da zai wakilce mu ya kasance daga karkara yake ba daga wani birni ko cikin Gari ba daga baki dayan yankin mu\”.

  Ya kara da cewa hakika a Cire masu duk wani Dan takarar da ya fito daga PDP ya shiga APC kasancewar Yan PDP ba tuba suke ba \” mu Yan PDP ne a da can don haka mun San ba tuba Dan PDP yake ba don haka ba zamu zabi tubabben PDP ba ya koma APC da Kowane irin suna yazo.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here