ZA  A GUDANAR DA ZABEN KANANAN HUKUMOMIN FILATO A RANAR 10 GA WATAN OKTOTA

0
483

 

 Isah Ahmed, Jos

HUKUMAR zabe mai zaman kanta ta jihar Filato  [PLSIEC] ta sanya ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa, a matsayin ranar da zata gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Filato. Amma hukumar ta bayyana cewa a cikin kananan hukumomi 17 da ake da su a jihar,  ba za a gudanar da wannan zabe ba, a kananan hukumomi guda hudu.

Wadannan kananan hukumomi da ba za a gudanar da zaben ba, sune  Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Barikin Ladi da Riyom, kuma ba za a gudanar da wannan  zabe bane a wadannan kananan hukumomi, saboda matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a wadannan wurare.

Shugaban hukumar zaben Mista Fabian Ntun ne ya bayyana haka, bayan kammala taron da ya yi da shugabannin jam’iyyu da ke jihar, a ranar talatar nan da ta gabata a garin Jos fadar gwamnatin jihar.

Idan dai ba a manta ba,  ita dai hukumar zavbn ta jihar Filato taso ta gudanar da wannan zabe, tun a ranar 17 ga watan fabarairu na shekara ta 2017 da ta gabata, amma hakan bai yiwu ba, saboda matsalar tsaro da ake fama da shi a jihar.

Kuma tun a wannan lokaci hukumar ta tantance ‘yan takarar  shugabannin  kananan hukumomin da kansiloli guda 725 daga jam’iyyu daban daban da zasu fafata a wannan zabe.

A yanzu dai kananan hukumomin da za a gudanar da wannan zabe sun hada da  Bassa, Bokkos, Jos ta gabas, Kanam, Kanke, Langtang ta Arewa, Langtang ta Kudu, Mangu, Mikang, Panshin, Quan-Pan, Shendam da kuma Wase.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here