Daga Yanzu Karatun Mata Kyauta Ne A Kaduna – Inji Gwamna El-Rufai 

0
541

 

Daga Usman Nasidi

A kokarinta na inganta ilimin mata, gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ta kaddamar da tsarin karatu kyauta ga mata da yan mata a makarantun jahar gabaki daya.

Gwamnatin ta sanar da haka ne a cikin wata takarda da ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha ta jahar ta fitar a ranar Laraba, 19 ga watan Satumba na shekarar 2018, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Takardar da ta samu sa hannun wakilin kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha ta jahar Kaduna, Umar Dabo Hussamatu ta shaida ma dukkanin daraktocin shiyyar ilimi na jahar Kaduna cewa daga zangon karatu na shekarar 2018/2019, dalibai mata yan aji hudu zuwa yan aji shida ba zasu biya kudin makaranta ba har ila masha Allah.

Idan za’a tuna tun a farkon gwamnatin El-Rufai ne ya soke biyan kudin makaranta ga dukkanin daliban jahar tun daga matakin Firamari zuwa matakin aji uku na karamar sakandari, sai ga shi kuma a yanzu an dauke ma dalibai mata na babbar sakandari kudin makaranta.

Daga karshe takardar ta gargadi dukkanin shuwagabannin makarantun sakandari jahar dasu tabbata sun yi biyayya ga wannan sabuwar dokar ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha ta gwamnatin jahar Kaduna.

Daga cikin ayyukan samar da cigaba ga sha’anin ilimi a wanda Gwamna El-Rufai ke yi a jahar Kaduna akwai ciyar da daliban Firamari, dinka ma dalibai kayan makaranta kyauta, sabunta makarantu a duk fadin jahar, gina sabbin makarantu, karin gine ginen azuzuwa a makarantu, daukan dubunnan ingantattun malamai da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here