Mustapha Imrana Abdullahi
Hukumar kula da hana sha da Fataucin miyagun Kwayoyi ta kasa reshen jihar Jigawa ta samu nasarar kamawa tare da lakatawa magungunan da suka Kai nauyin Tan Shida da digo ashirin da daya.
Shugabar hukumar reshen Jigawa Uwargida Josephine Obi ta shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa an gudanar da aikin ne a ranar shida ga watan Satumba a birnin Dutse daga hannun masu safarar Kwayoyi.
Ta ce daukar wannan mataki ya biyo bayan irin dokar da babban mai shari\’a na babbar kotun Jihar Jigawa ya saka ne a Dutse.
Kwamandar ta kara da cewa daga shekarar 2013 sun samu nasarar Kama mutane dubu 3,608 da ake zargi an kuma Kwace Kwayoyi da sauran kayan Maye da yawa masu nauyin Tan dari 8.26.
Wanda tuni aka yankewa mutane da suka Kai dari 753 hukuncin da ya Kai su gidajen yari daban daban.
\” Mun Kuma samu gabatar da tarurrukan fadakar wa da na kara wa juna Sani a kan batun illar Kwayoyi\”.
\”Dukkan mai shan Kwayoyi muna bashi shawarwarin da suka kamata, a wannan rundunar\”.
Sai da Muka gargadin ta da cewa rundunar ba za ta amince da a sabawa dokar hana sha da safarar miyagun Kwayoyi ba ko kadan.