Hukumar SEMA Ta Rarraba Kayan Tallafi Ga Al\’ummar Da Iftila\’in Ruwa Ya Abkawa

0
471
PIC.4. NEMA OFFICIAL ADDRESSING SOME INTERNALLY DISPLACED PERSONS (IDPS) IN LAMURDE LOCAL GOVERNMENT AREA OF ADAMAWA STATE ON SATURDAY 19/5/12).

 

DAGA MUHAMMAD SANI CHINADE, DAMATURU

HUKUMAR kai daukin gaggawa (SEMA) dake Jihar  Yobe  ta rarraba kayayayyakin tallafin da kudadensu ya kai kimanin Naira Miliyan 120 ga al\’ummomin da iftila\’in barnar ruwan sama ya fadawa a wasu unguwannin garin Damaturu.

Da ya ke jawabi ya yin mika kayayyakin tallafin a garin Damaturu babban sakataren ma\’aikatar ta SEMA Alhaji Musa Idi Jidawa ya bayyana cewar kafin nan sai da suka kafa kwakkwaran kwamitin da ya kunshi wasu jami\’an hukumar ta SEMA da na Masarautar Damaturu da kuma na karamar hukuma don zakulo wadanda wannan iftila\’i ya fi shafa da suka fi cancanta da samun wannan tallafi.

Alhaji Musa jidawa ya kara da cewar akalla magidanta kimanin 595 ne aka gano wannan iftila\’i ya fi shafa kai tsaye, kuma kowane mutun an kididdige irin mizanin asarar da ya yi.

Sakataren ya kuma godewa gwamna Ibrahim Gaidam dangane da kokarin da ya yi na daukar matakin gaggawa na bada umarnin kai tallafi ga wadannan al\’ummomi da iftila\’in barnar ruwa ta fadawa.

Alhaji Musa Jidawa ya ci gaba da cewar, don ganin an samu daidaito ga wannan kaso na rarraba wadannan kayayyaki na tallafi an samar da karin kwamitin mutane 5 da suka hada da Bulama da Limamai da kuma mata guda 2 da matasa  da wannan iftila\’i ya shafa don an ganin an rarraba kayayyakin tallafin cikin sauki.

Daga nan sai ya roki wadanda suka amfani da wannan tallafi da su yi amfani da shi ta hanyoyin da suka dace wajen sake ginawa da rufa gidajensu. Kana su guji sayar da su kamar yadda wasu ke da al\’adar yin haka.

Shima a nasa jawabin shugaban karamar hukumar Damaturu Alhaji Bulama Bukar yabawa ya yi ga gwamnatin Jihar Yobe dangane wannan tallafi da ta baiwa wadannan al\’ummomi da suka hadu da iftila\’in ta\’adin ruwa. Don haka ya kirayi mambobin kwamitin da su yi aiki bil-hakki da gaskiya yayin rarraba wadannan kayayyaki don kaucewa zarmiya.

A jawabinsa mai marttaba Sarkin Damaturu wadda Wazirin masarautar Alhaji Maisanda Lawan ya wakilta godiyarsa ya nuna ga gwamna Ibrahim Gaidam dangane da wannan hobbasa da ya yi na bada wannan tallafi, kana ya hori magidantan da su kaucewa sayar da wadannan kayayyaki da aka basu.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka rarraba sun hada da bandira 1975 na kwanan rufi da kuma buhuna 1975 na siminti sai kuma barguna dubu 1990 hade da tabarmi adadin hakan. Kana akwai kuma turaman zannuwa, bokatai da makamantansu.

Sauran kayayyakin sun hada da katakan rufi kimanin dubu 12,700 da kuma fallayen silin guda dubu 5390 sai kwalayen kusar rufi guda 601 da kuma manyan robobin fenti guda dubu 3775.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here