Na Fito Takara Domin Na Warware Matsalolin Kasar Nan Ne – Inji Dokta Attahiru Bafarawa

  0
  648

   

  YAYINDA \’yan siyasa masu Neman mukamai daban-daban suke yawon tuntubar magoya bayansu suke nuna masu manufofinsu, dan takarar shugaban kasa Karka shin jamiyyar PDP dokta Attahiru Dalhatu bafarawa ya shaidawa cewa domin ya gyara matslolin kasar ya ne yasa ya daura damarar shiyasa tafiya kowace kusurwar kasar nan a mota ba kamar yadda wasu masu yawo a jirgin sama suke YI ba suna kamfe.

  Ga kuma yadda hirarsu da wakilinmu a kalaba Musa muhammad Kutama ta kasance.

  Gtk: ka gamsu da yadda gwamnatin APC take.cewa ta kawo Canji a kasar nan shekara uku da hawan su mulki?

  Dokta Attahiru bafarawa: to ai ba maganar na gamsu bane ko ni ban gamsu ba bane jama\’ar najeriya ne basu gamsu ba ko ban gamsu ba don ba a ga Canji ba amma anga na wahala eh !anyi Canji na wahala saboda haka shi yasa jam\’iyyar PDP matsayinmu masu takarar shugaban kasa yasa muke so muga mun tsaya munga mun kawar da wannan Canji na bakar wahala da APC ta kawo mana.

  Gtk: Wannan shi ne karo na farko da ka fito takarar mukamin shugaban kasa a jam\’iyyar PDP meyasa ka yanke shawarar fitowa takara?

  Dokta Dalhatu bafarawa: don ina ganin na cancanta matsayina na dan najeriya kuma dan siyasa nasan wahala da halinda kasar mu take ciki bakin gwargwado saboda ilimin da nake dashi Dana mulkin jihar sakkwato da na yi Wanda jama\’a sun shaida kowa ya gani kaga idan na samu dama aka bani dama aka amince mini zan dauko irin wadannan abubuwa dana dauko na raya kasa da kasarmu gaba daya shi yasa na gaya ma ka na fito neman mukamin.

  Gtk: A jamiyyar PDP mutane da dama sun fito neman takarar shugaban kasa idan jam\’iyya tace Ku hadu a sasanta abarwa mutum daya idan aka gayyace ka za ka je kuma ka amince?

  Dokta Attahiru bafarawa: ni ina ganin duk wannan abu ba abin matsuwa bane abin alfahari ne abar jam\’iyyar da dan najeriya ya fito neman wannan kujera ya cancanta ya fito neman takara ya bada gudunmawarsa idan aka tsayar da ni ina ga wannan ba abin damuwa bane kowa aka  tsayar wannan ba abin.damuwa ba ne.

  .Gtk:ta wace gaba ka ke jin zaka fara gyaran matsalar da ku ke zargi APC ta haifar ?

  Dokta Attahiru Dalhatu: to abinda.zanfara gyara shi ne hadin kan yan kasa da yan najeriya gaba daya da kuma abinda yan najeriya ke son kirana anan shi ne duk wanda ke son takarar shugaban kasa bai dace ba ace hana yawo a jirginsa ba yana kamfe ba yana yawo kamar tsuntsu, kamata yayi yazo ta kasa kudu da arewa suke fama da matsalar hanyoyi kamata yayi ya zaga a mota yaga yadda hanyoyin da suka lalace shi yasa kaga na.dauki zagaye a mota tun daga kudu maso gabas gashi yanzu ina kalaba kudu maso kudu na zabi in zaga da kafata domin inganewa idona masalolin jama\’a idan an zabe ni shugaban kasa nasan matsalar ko ina ba sai wani ya gaya min ba najeriya yanzu ta zama mazaba ta ta yadda zan iya gyara ko\’ina idan hakan ya taso.

  Gtk ana ta cecekucen sake fasalin kasa idan Allah ya baka mulki zaka yadda afasalta kasar nan?

  Dokta Attahiru Dalhatu: ai wadan nan abubuwan duk ra\’ayin mutane ne duk Wanda.yake so akawo gyara sai yazo a zauna dashi don aji wani irin  gyara ko canji yake so akawo.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here