Isah Ahmed, Jos
MAI martaba Sarkin Saminaka da ke jihar Kaduna Alhaji Musa Muhammad Sani, ya nada fitattacen dan Najeriya nan da ke zaune a kasar Amerika, kuma mai yin sharhi kan kasar ta Amerika a kafofin watsa labaran duniya, Alhaji Garba Sulaiman Cracko Saminaka a matsayin sabon Madakin Saminaka, ranar juma’ar da ta gabata a fadarsa da ke garin Saminaka.
Da yake jawabi a lokacin nadin, Mai martaba Sarkin na Saminaka Alhaji
Musa Muhammad ya bayyana cewa an nada sabon Madakin ne sakamakon rasuwar tsohon Madakin na Saminaka Alhaji Ibrahim Sani [Dan Tsoho] shekara daya da ta gabata.
Har’ila yau ya ce an nada Alhaji Garba Sulaiman Saminaka a matsayin sabon Madakin na Saminaka ne, ganin irin kishin da yake da shi ga masarautar ta Saminaka.
‘’Ganin irin taimakon da sabon Madakin yake yiwa mutanen wannan masarauta da zumuncin da yake yi a wannan gari na Saminaka, ya sanya masarautar ta duba taga ya da ce a bashi wannan sarauta. Don haka muna fatar zai cigaba da bada gudunmawa wajen daukaka wannan masarauta da al’ummarta gabaki daya’’.
Da yake zantawa da wakilinmu bayan kammala nadin, sabon Madakin na Saminaka Alhaji Garba Sulaiman Saminaka ya bayyana matukar farin cikinsa da godiyarsa ga Mai martaba Sarkin Saminaka, da masarautar Saminaka kan wannan nadi na Madakin Saminaka da aka yi masa.
Ya ce marigayi tsohon Madakin Saminaka Alhaji Ibrahim Sani kani ne a wajensa kuma mutum ne wanda a lokacin da yake raye, kullum yana kokarin yaga ya kawo wani abu na cigaba a wannan masarauta.
Sabon Madakin ya ce babban abin da yake son ya yi don cigaban wannan masarauta, shi ne zai cigaba da taimakawa matasan wannan masarauta.
‘’Zamu zauna da matasan wannan masarauta mu tarbiyartar dasu mu ilmintar dasu domin su sami abin da zasu dogara da kansu. Kuma zamu je duk inda ya kamata muje, don ganin an taimakawa matasan wannan masarauta. Kuma zan bayar da gudunmawata wajen ganin an cigaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan masarauta’’.