Babbar Jami’a Mafi Inganci A Duniya Ta Nada Gwamnan Jahar Kaduna Muhimmin Mukami

0
582
Gwamna Malam Nasir El-Ruffa\'i na Jihar Kaduna

 

Daga Usman Nasidi

BABAN jami’ar Duniya mafi inganci kuma jami\’a ta biyu da tafi dadewa a Duniya, Oxford ta sanar da nadin gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin guda daga cikin mambobin kwamitin koli, watau iyayen cibiyarta na yankin nahiyar Afirka.

Jami’ar Oxford za ta rantsar da wannan kwamitin mai dauke da mutane Tara da zai dinga bata shawara akan yadda za ta gudanar tare da tafiyar da cibiya ta Afirka a ranar 12 ga watan Oktoba.

Aikin wannan kwamiti shi ne daura cibiyar akan tsare tsare daban daban da kuma kulla kyakkyawar alaka tsakaninta da gwamnatocin kasashen Afirka, cibiyoyi da kuma yan kasuwa da kasuwancin Afirka.

Haka zalika ana sa ran mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne zai kaddamar da wannan kwamiti.

Jami’ar ta nada Tito Mboweni, bakar fata na farko daya fara shugabantar babban bankin kasar Afirka ta kudu, kuma tsohon ministan kwadago a zamanin mulkin Nelson Mandela a matsayin shugaban kwamitin,

sauran yayan kwamitin sun hada da: Gwamna Nasir El-Rufai Alex Duncan, daga kasar Birtaniya Ivor Agyeman-Duah, daga kasar Ghana Ministan harkokin kasashen wajen Najeriya.

Uwargidar shugaban kasar Namibia, Madame Monica Geingos Gareth Ackerman, shugaban kamfanin Pick’n Pay daga kasar Afirka ta kudu Dakta Charlotte Harland-Scott, uwargidar tsohuwar shugaban kasar Zambia Farfesa Ibrahim Gambari, tsohon mataimakin sakataren majalisar dinkin duniya Linda Mabhena-Olagunju, shugaban kamfanin DLO Energy Group (Pty) Ltd, daga kasar Afirka ta kudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here