Gwamnonin Da Suke Bayar Da Hutun Shigowar Shekarar Musulunci Sun Yi Daidai-Sheikh Jingir

0
889

 

Isah Ahmed, Jos

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa gwamnonin jihohin da suke bayar da hutun murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci a Najeriya sun yi daidai.

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida, kan mahimmancin ranar 1 ga watan Almuharram na  shigowar sabuwar shekarar musulunci ta shekara ta 1440.

Ya ce duk gwamnonin jihohin Najeriya da suke  bayar da hutu a ranar 1 ga watan Almuharram sun yi daidai, basu yi kuskure ba. Domin sun zo sun tarar da yahudawa sun kakabawa musulmi  hutun ranar 1 ga watan Janairu na kowace  shekara, wanda ba musulunci bane da sauran ranakun hutu wadanda duk ba musulunci ne ya ce ayi ba.

Ya ce a wajen musulmi 1 ga watan Almuharram shi ne ranar 1 ga watan sabuwar shekarar musulunci. Don haka ya yi daidai a sanar da duniya cewa watan Almuharram ya kama, kuma a  kawowa ma’aikata sauki a wannan rana. Don haka ya yabawa  gwamnonin da suke bayar da wannan hutu.

Sheikh Sani Yahya ya yi bayanin cewa Watan Almuharram shi ne na daya a watannin musulunci guda 12, wadanda Allah ya ambata  a cikin Alqura’ani mai girma. Kuma  da lissafin wadannan  watannin musulunci ne, musulmi suke Azumin watan Ramadan da aikin hajji  da gane tafiyar lokaci.

‘’Babban abin lura a nan, shi ne watan Almuharram wata ne mai daraja wanda Allah ya hana zalunci a cikinsa,  kuma ya ce duk  aikin da zamu yi, muyi aikin da  ya ce ayi. Idan watan ya kai  ranar 9 da 10 sunnah ce ta Manzon Allah SAW ayi  Azumin Tasu’a  da Ashura. Kuma a ranar Ashura mu ciyar da ‘yayanmu da matanmu da haularmu’’.

Sheikh Jingir ya yi  kira ga musulmi kada su yi wasa da Azumin nan na Tasu’a da Ashura da sauran addu’o’i a wannan wata domin sunnah ce mai karfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here