Isah Ahmed, Jos
Daraktan sabuwar makarantar nan ta Asasul Islam Model Private, ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa da ke unguwar Randar ruwa Rikkos a garin Jos babban birnin jihar Filato,
Ustaz Muhammad Muhammad Abubakar ya bayyana cewa bisa tsare tsaren da suka yiwa wannan makaranta, da yardar Allah zata zama abin koyi ga dukkan makarantun kungiyar dake ciki da wajen Najeriya. Ustaz Muhammad Muhammad Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce a wannan sabuwar makaranta mai azuzuwa 12 da ofisoshin gudanarwa da wani bawan Allah, Alhaji Abubakar Sulaiman ya gina, kuma ya baiwa wannan kungiya ta kasa, suna son su gudanar da makarantar kananan yara da firamare da sakandire.
Har’ila yau ya ce suna son da yamma su rika karantar da tarbiyar musulunci a wannan makaranta, da sanin makamar harshen larabci da haddar Alkura’ani mai girma, da mahimman abubuwa kan addinin musulunci.
Hakazalika ya ce zasu rika gabatar da karatun asabar da lahadi don matan aure da magidanta, da basu riga sun yi karatuttukan addinin musulunci ba.
Ya ce mutum ko ya yi karatun boko, yaje har jami’a ya yi digiri, akwai bukatar yazo ya yi karatun addini. Don haka a wadannan ranaku na asabar da lahadi zasu rika karantar da matan aure da safe kuma su karantar magidanta da yamma.
‘’Abin da ya karfafa mana gwiwar kawo wadannan sababbin tsare tsare a wannan makaranta shi ne dama muna da irin wadannan makarantu na Asasul Islam a dukkan fadin Najeriya.
Don haka ne muke son mu mai da wannan makaranta ta musamman da zamu inganta harkokin koyarwa ta hanyar samar da kayayyakin aiki irin na zamani, da koyar da ilmin kwanfuta da ilmin kimiyya da samo kwararun malamai don ganin daliban wannan makaranta sun sami ingantatcen ilmi. Domin mu nunawa sauran makarantunmu a aikace aikacen da suka kamata su yi’’.
Ustaz Muhammad Muhammad ya yi bayanin cewa suna son suyi tafiya daidai da zamani, ta yadda daliban da suka sami shiga wannan makaranta, zasu rika fita da abubuwan da ya kamata don wucewa makarantun gaba kamar jami’o’i da sauran manyan makarantu batare da wata matsala ba.
Ya yi kira ga al’umma su basu goyan baya da hadin kai, don su sami nasarar cimma kudurori da suka sanya a gaba.