2019: APC TA HARAMTAWA MAMA TARABA TAKARAR GWAMNA

  0
  898

   

  Daga Usman Nasidi

  JAM\’IYYAR APC mai mulki ta haramtawa wasu \’ya\’yanta shiga takarar gwamna ciki har da ministan harkokin mata, Aisha Alhassan da ministan sadarwa, Adebayo Shittu

  Kwamitin gudanarwan na jam\’iyyar ne ta dauki wannan matakin sakamakon rahoton da da samu daga kwamitin tantance \’yan takarar gwamna na jam\’iyyar.

  Uwargida Aisha, wadda aka fi sani da Mama Taraba tana son takarar kujerar gwamna na jihar Taraba ne yayin da Mrista Shittu Adebayo shi kuma yana niyyar takarar gwamna ne a jihar Osun

  Duk da cewa kwamitin ta soke takarar Mr Shittu ne saboda bashi da shaidar kammala NYSC ko kuma hidimar kasa, kwamitin ba ta bayar da dalilin ta na soke takarar Mrs Alhassan ba.

  Wasu masu neman takarar gwamnan da kwamitin bata tantance sun hada da Osiobe Eric Okotie (Delta), Ejikeme Ugwu (Enugu), Ibrahim Mohammed Mera (Kebbi), Danladi Envulu-Anza Halilu (Nasarawa) da Abubakar Mamma Jiya Maaji (Niger).

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here