Gwamnoni 4 Sun Yiwa Fursinoni 340 Afuwa A Najeriya

0
511

 

Rabo   Haladu Daga Kaduna

GWAMNONIN Najeriya hudu sun yi afuwa ga fursunoni akalla 340 albarkacin cika shekaru 58 da  amun ‘yancin kai daga turawan Birtaniya.

Gwamnonin sun hada da Abubakar Bello na Niger da Nasir El-Rufa’i na Kaduna da Simon Lalong na Filato da kuma Muhammadu Bindow na Adamawa.

Gwamna Bello ya yi afuwa ga fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa, yayin da ya sassauta wa wasu hukuncin kisa zuwa hukuncin zaman gidan kaso na wani dan lokaci.

Gwamnan ya kuma sallami wasu fursunoni 40 tare da bada umarnin biya wa fursunoni 221 tarar da aka ci su na kudade.

Shi kuwa Gwamna El-Rufai na Kaduna, ya yi afuwar ne ga fursunoni 24 da suka hada da wadanda aka yanke wa hukucin kisa kamar yadda ya shaida wa jama’a a yayin faretin da ya gudana a filin wasa na Ahmadu Bello da ke jihar don tunawa da ranar samun ‘yancin.

A can Adamawa kuwa, Gwamna Bindow ya yi afuwa ga mutane 22 kamar yadda sanarwar  ta fito daga Kwashinan Yada Labarai, Ahmad Sajo ya bayyana, yayin da Gwamna Lalong na Filato ya yi afuwa ga fursunoni 7 albarkacin wannan rana ta 1 ga watan Oktoba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here