Kisan Janar Alkali: An Damke Yan Birom 30 Da Muggan Makamai A Garin Du

0
620

Daga Usman Nasidi

YAYINDA ake cigaba da nema gawan Janar Alkali, Hukumar sojin Najeriya sun fara binciken wadanda ake zargi da kisan jama\’a a Du, karamar hukumar Jos ta kudu.

An damke mutane 30. Hukumar sojin kasan Najeriya ta saki jawabin ne da yammacin yau Laraba, 3 ga watan Oktoba 2018 kan irin mutanen da aka kama makamai.

Jawabin yace: “Yayinda muke cigaba da ceto Manjo Janar IM Alkali (Mai mirabus), babban hafsan sojin kasan Najeriya ya nada runduna ta musamman domin sanin ainihin inda yake.

Farawa da iyawa, jami’an sojin sun yiwa garin Doi Du zobe a karamar hukumar Jos ta kudu inda suka damke mutane 30.”

Daga cikin makaman da aka kama a hannunsu shine: Bindigogin gargajiya 3, kananan bindigogi 3, 5 X 7.62 MM(SP) RDS, 30 X 9MM RDS,wukake, takubba, takalman soji, katin shaidr yan banga, Babura 5.

Keke Napep 1, da sauransu. Za mu cigaba da aiki har sai mun nemi babban hafsan.”

Bayan gano motar babban hafsan a cikin teku a garin, an gano wasu motoci akalla 13 a cikin harda babbar motan haya.

Mun kawo muku rahoton cewa Al’ummar garin dake garin Du dake karamar hukumar Jos ta kudu sun fara tserewa daga garin nasu don tsoron hukuncin da kan iya hawansu sakamakon gano motar wani babban jami’in Soja da aka yi a cikin wani korama dake garinsu, kuma an nemi sojan an rasa.

Wata ma’abociyar kafar sadarwar zamani, Zara Gift Oyinye ce ta daura hotunan matan garin yayin da suke ficewa daga garinnasu zuwa wasu sassan jahar Filato don tsira daga hukuncin da suke tunanin zai iya hawansu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here