Yan Sanda Sun Rufe Sakatariyar APC Bayan Fusatattun Matasa Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja

0
517

  Daga Usman Nasidi

JAMI’AN tsaro sun rufe sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki biyo bayan wani zanga-zanga da matasa suka yi akan yin amfani da zaben fidda gwani na wakilai wajen tsayar da dan takarar sanat na babba bhirnin tarayya.

Fusatattun matasa da ake ganin magoya bayan daya daga cikin yan takarar dake neman tikitin takarar kujeran sanata a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a birnin tarayya Abuja sun mamaye babban sakatariyar APC na kasa inda suke gudanar da zanga-zanga.

A cewar masu zanga-zangar yin amfani da zaben fidda gwani na wakilai daidai yake ga cewar dan asalin yankin ba zai samu tikitin ba.

Matasan dake dauke da muggan makamai daban-daban sun rufe mashigi da hanyar fita na unguwar Blantyre inda anan ne sakatariyar yake.

A halin da ake ciki, rahotanni na bayyana cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ahmad Lawan a ranar Laraba, 3 gawatan Oktoba ya mallaki tikitin jam’iyyar Progressives Congress (APC) domin takarar kujerar sanata a yankin Yobe ta arewa a zabe mai zuwa.

Alhaji Umar Kareto, jami’an zaben yace wakilai 1,865 aka tantance a mazabar shugaban majalisar inda ya samu kuri’u 1,702 yayinda aka soke 12.

Lawan wanda ya fito bai da abokin hamayya yayi godiya ga mutanen da suka amince da shi domin ya wakilci yankin a majalisar dattawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here