Halin Da Ministan NeJa Delta Ya Nuna Baiyi Dattaku Ba -APC

  0
  489

  Musa Muhammad Kutama daga kalaba

  JAM\’IYYAR APC a jihar kuros riba ta bayyana rashin jin dadin ta game da raba kan jamiyya da \’yan jam\’iyyar da ministan neja delta fasto Usani Uguru Usani yayi inda ta bayyana lamarin da hali na rashin dattaku.

  Matthew Achigbe shugaban jamiyyar a kuros riba ne ya sanar da haka ga manema labarai a ranar laraba a harabar ofishin jamiyyar.

  Shi dai ministan, jam\’iyyar na zargin sa ne da ware wasu yan jam\’iyyar ya bude nasa ofishin ya gudanar da nasa zaben fidda gwani takarar gwamna ya yi shelar shi ne ya lashe zaben.

  Idan za\’a iya tunawa sakamakon zaben fidda gwani ya nuna, Sanata John owan enoh, ne ya lashe zaben da yawan kuri\’u dubu 82, da metan yayinda shi kuma Usani Uguru Usani ya samu yawan kuri\’u dubu 17 da 77 yazo kurar baya a jerin wadanda sukayi takarar a.zaben neman mukamin gwamna a jam\’iyyar.

  Achigbe yaci gaba da cewa \” halin rashin dattaku da Usani Uguru Usani ya nuna na warewa daga cikin yan jam\’iyya ya gudanar da zaben fidda gwani, sannan ya Sanar wa yan jarida shi ne ya lashe zaben wannan rashin dattaku ne da kuma yiwa demkradiyya da APC Kama karya lamarin da ba zamu yadda dashi ba.\”inji shi

  Hakan kuma shugaban jamiyyar APC tace, ta nada kwamitin sulhu domin a sasanta ragowar yan takarar da ba su yi nasara ba suzo a tafi tare wanda yaki yadda a tafi tare kuma yaki za\’a dauki mataki a kansa.

  APC, ai tace ita ta gamsu da kwamitin zartarwar jam\’iyyar karkashin jagorancin Alhaji Aliyu magaji ya gudanar da zaben fidda gwanin ya kuma tabbatar da nasarar John owan enoh a matsayin wanda ya yi nasara a zaben kamar yadda jadawalin kundin zabe na jam\’iyyar APC sashe na 13.4 (xiv) ya tanadar .
  Jamiyyar ta sha alwashin ladabtar da Usani Uguru Usani idan bai yi mata da\’a ba ta kuma garkame ofin sa na APC daya kafa.

  Yan takara biyar ne suka fafata a neman mukamin gwamna da suka hada da ministan Neja Delta Usani Usani, John Owan Enoh, da Edem Duke sauran sune John Ukpan da Eyo Etim Nyong.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here