Jam\’iyyar APC Ta Tabbatar Da Shehu Sani A Matsayin Dan Takarar Da Ta Wanke

  0
  495

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  BAYANAN da ke fitowa daga bakin kakakin Jam\’iyyar APC na kasa Yekini Nabena bayyana cewa izuwa yanzu Kwamared Sanata Shehu Sani ne Jam\’iyyar ta wanke a matsayin Dan takarar shiyyar Kaduna ta tsakiya.

  Kakakin APC Yekini Nabena ya tabbatar wa manema labarai hakan ne a zantawar da aka yi da shi ta wayar salula daga kaduna.

  Inda ya tabbatar wa manema labaran cewa a halin yanzu abin da APC ta sani shi ne sanata mai ci Shehu Sani, ne wanda aka wanke ya zama Dan takarar Sanatan shiyyar Kaduna ta tsakiya.

  Ya kuma yi kira ga daukacin al\’ummar baki daya da cewa \”su yi watsi da dukkan wani labarin da yake yaduwa da cewa jam\’iyyar APC ta wanke Uba Sani\”.

  Indai za a iya tunawa dangantaka dai tayi tsaki ne tsakanin Sanata Shehu Sani da Gwamna Nasiru El-Rufa\’i ne tun a watan Maris lokacin da majalisar Dattawa ta dakile batun maganar cin bashin kudi Dala miliyan Dari uku da hamsin da Jihar Kaduna ta kammala Shirin karbowa daga bankin duniya.

  Kamar yadda bayanai suka tabbata, an yi yarjejeniya cewa tun da sanata Shehu Sani ya yi zamansa a APC ba tare da canza wa kamar yadda wasu suka yi za a bashi damar tsayawa takara kai tsaye daga APC, wato sakayyarsa ta rashin komawa PDP kamar yadda wadansu suka yi.

  Kamar yadda wakilinmu ya tattaro batun kin wanke wadansu da za su yi takara karkashin jam\’iyyar ya haifar da yawan zanga zanga da korafe korafe, inda har wasu Gwamnonin APC suka ziyarci shugaba Buhari a fadar shugaban kasa domin bayyana masu korafin su a ranar Alhamis da ta gabata.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here