Atiku Zai Kawo Chanji Na Gaskiya  A Kasarnan-Inji Musa  Chaye

  0
  774

  JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

  AN bayyana cewa Nijeriya zata sami chanji na gaskiya idan aka zabi Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa a zaben shekara ta 2019 da ake shirin gudanar wa.

  Wannan bayani ya fito ne daga bakin wani makusanci ga dan takarar shugabancin kasar watau Alhaji Musa Yola wanda aka fi sani da Musa Chaye cikin zantawarsu da wakilin mu bayan kammala zaben fitar da gwani na yan takarar shugabancin kasa a tutar jam\’iyyar PDP.

  Musa Chaye yace Atiku Abubakar mutum ne mai son ci gaban kasarnan don haka nema yake ta kokarin samun cikakkiyar damar yin abubuwa na alheri  domin tabbatar da wannan buri nasa na kyautata rayuwar al\’umar kasa.

  Sannan ya sanar da cewa Atiku Abubakar ya rike mukamai masu tarin yawa kuma yasan matsalolin kasarnan da kuma hanyoyin warware su, don haka yana dakyau al\’umar Nijeriya su zabe shi a matsayin shugaban kasa domin kawo sauyi mai amfani ta kowane fanni na zamantakewar su batare da nuna bambanci ba.

  Alhaji Musa Yola ya kuma  jaddada cewa zasu ci gaba da bayyana sahihancin Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar ta yadda kowane dan kasa zai fahimci kyawawan halayensa da kuma manufofin sa na bunkasa wannan kasa tamu, tareda yin godiya ta musamman ga wakilan da suka tabbatar dashi a matsayin dan takarar shugabancin wannan kasa a  jam\’iyyar PDP.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here