An Yi Gangami A Zaria Domin Yi Wa Gwamnan Kaduna El-Rufai Sallar Tsinuwa

0
579

Daga Usman Nasidi

MUN samu labari cewa an yi Jam’i a cikin garin Zaria da ke Kaduna domin yi wa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai sallar tsinuwa a dalilin korar dinbin Ma’aikata da yayi daga aiki a Gwamnatin sa.

Kamar yadda labari ya zo mana, Jama’a sun yi cincinrindo ne a babban Masallacin idi da ke cikin Garin Zaria inda su ka rafka addu’o’i ga Ubangiji domin wannan Gwamnati mai-ci a Jihar Kaduna ta kai kasa a zabe mai zuwa.

Mutanen wanda yawancin su Ma’aikatan Gwamnatin Jiha ne da Mai Girma Gwamna Nasir El-Rufai ya sallama daga aiki a kan wasu dalilai sun koma wajen Ubangiji su na neman Gwamnan ya sha kasa a zaben badi na 2019.

Gwamnatin APC ta Malam Nasir El-Rufai dai ta sallami dinbin Ma’aikata aiki a Jihar Kaduna a kokarin da ta ke yi na tsabtace harkar ilmi da kuma yi wa Kananan Hukumomi da sauran Ma’aikatan Jihar garambawul din da ya dace.

Kwanaki dai Ma’aikatan da aka raba da hanyar cin abincin su, sun yi irin wannan salloli inda su ka rika kiran sunan Gwamna mai-ci su na bin sa da tsinuwa. Kawo yanzu dai an kori Malaman makaranta kurum sama da 25000 aiki.

Kwanan nan kun ji cewa Gwamnatin El-Rufai ta maida karatun Boko ya zama kyauta a kaf fadin Jihar Kaduna ga Matan da ke mataki na Sakandare. Wannan yunkuri dai ya jawowa Gwamnan abin yabo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here