JERIN SUNAYEN MUTANE 50 DA BUHARI YA HARAMTAWA FITA DAGA NAJERIYA

0
600

Daga Usman Nasidi

A JIYA Asabar, shugaba Muhammadu Buhari ya saki jawabi da ya kidima mutanen Najeriya kan mutane akalla hamsin da ake zargi da cin hanci da rashawa. Ya bada umurnin haramta musu fita daga Najeriya.

Shugaban kasa ya bada wannan umurni ne bayan kotu ta tabbatar da cewa yanada ikon rike dukiyoyin dukkan wanda ake zargi da rashawa.

Cikin wadanda wannan abun ya shafa sune Tsaffin gwamnonin Najeriya 14, tsaffin ministoci bakwai, tsaffin sojoji shida, tsaffin alkalai biyu, da wasu yan siyasa. Karanta jerin sunayensu

Daga cikin tsofaffin gwamnoni sun hada da, Saminu Turaki (Jigawa), Murtala Nyako (Adamawa), Adebayo Alao-Akala (Oyo), Gabriel Suswam (Benue), Rasheed Ladoja (Oyo), Orji Uzor Kalu (Abia), Danjuma Goje (Gombe), Attahiru Bafarawa (Sokoto), Muazu Babangida Aliyu (Niger).

Chimaroke Nnamani (Enugu); Sule Lamido (Jigawa); Gbenga Daniel (Ogun); Ibrahim Shehu Shema (Katsina). Ahmadu Fintiri (Adamawa) Tsaffin ministocin: Nenadi Usman, Bashir Yuguda, Jumoke Akinjide; Bala Mohammed; Abba Moro; Femi Fani-Kayode;

Sai tsofaffin sojoji sun hada da, Kanal Sambo Dasuki; Air Marshal Alex Badeh; Vice Admiral A. D. Jibrin; Air Marshal Mohammed Dikko Umar; Sunday Ehindero Air Marshal Adesola Amosu;

Hakazalika tsoffin Alkalai sune: Justice Rita Ofili-Ajumogobia; Justice Innocent Umezulike kana sauran yan siyasan sune: Shugaban tashar AIT Raymond Dokpesi Waripamowei Dudafa Olisa Metuh; Jide Omokore; Ricky Tarfa Dele Belgore (SAN).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here