ATIKU BA ZAI ZAMA SHUGABAN KASA BA – KAILANI

  0
  586

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  SHUGABAN Kungiyar a kasa a tare a raka na kasa Injiniya Kailani Muhammad ya bayyana dalilin da zai hana tsohon Mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya Mulki Nijeriya.

  Shugaban a kasa a tsare Injiniya Kailani Muhammad ya bayyana cewa babu ta yadda za a iya hadawa tsakanin BUHARI da Atiku, domin wutsiyar Rakumi tayi nesa da kasa, Kuma duk kan matakansa musamman tushen siyasar sa duk gurbace suke da zarge zargen cin hanci da rashawa.

  Shugaban na a kasa a tsare Injiniya Kailani Muhammad ya bayyana hakan ne a farin manema labarai a kaduna, inda ya bayyana batun kasance war Atiku a matsayin Dan takarar shugaban kasa na PDP da cewa abin Murna ne a Gare su.

  Kailani ya ce \” babban muhimmancin al\’amarin dai a nan shi ne Mafi yawan Yan Nijeriya sun San cewa Atiku Abubakar ba ta yadda zai zama tsaran shugaban kasa Muhammad BUHARI da aka zaba a shekarar 2015 kuma babu wata tantama za a sake zabensa a zaben 2019 Mai zuwa musamman saboda irin nagartarsa musamman a kan batun cin hanci da karbar rashawa ga kuma wata nagartarsa a kan kokarin farfado da tattalin arzikin kasa\”.

  Ya bayyana cewa Amma shi tsohon Mataimakin shugaban kasa kadin ya samu damar tsayawa Dan takarar PDP ya yi takara har sau hudu ba tare da samun nasara ba, \”duk da haka ba shi ne wanda ya dace ya shugaban ci Nijeriya ba a wannan lokacin saboda Yan Nijeriya sun bayyana matsayin su\”.

  Kailani ya ci gaba da bayanin cewa hidimar siyasa a halin yanzu wani babban al\’amari ne don haka ya da ce Atiku da ire iren mutanensa su Sani mulkin Nijeriya ba na sayar wa  bane.

  Ya kuma tantance cewa irin nasarar da shugaban kasa Muhammad BUHARI ya samu a cikin shekarar uku wani al\’amari ne da Saurabh Gwamnatocin da suka gabata ba su samu ba a cikin shekarun da suka gabata musamman wadanda suka yi shekaru Sha shi da suna jan jarensu a kan karagar mulkin kasa

  \”Wuraren da Gwamnatin ta samu nasarar sun hada da farfado da tattalin arzikin kasa, kokarin farfado da bangaren samar da gasket wutar lantarki,Ilimi da bunkasa duk kan al\’amuran yan Nijeriya da sauransu.

  \”Wani babban al\’amari shi ne Muhammadu BUHARI na kokarin farfado da tattalin arzikin kasa da mutuncin kasar a idan in  duniya baki daya, kuma wannan al\’amarin ne mutane da yawa ba su san a sani balantana jama\’ar kasar da na waje su Sani\”.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here