Gwamnatin Buhari Tana Kokari  Wajen Bunkasa  Noma A Kasarnan

  0
  639

  JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

  WANI babban manomi daga garin Gwarzo ta jihar kano Alhaji Maikudi Gwarzo yace ko shakka babu  gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana kokari kwarai wajen inganta noma rani da damina a kowane lungu dasako na wannan kasa.

  Yayi wannan tsokaci ne yayin tattaunawa da wakilin mu a wasu daga cikkn gonakin sa dake garin  na Gwarzo, tareda tabbatar da cewa Nijeriya zata iya ciyar da al\’umar ta abinci  harma ta kai wasu kasashe domin bunkasa cinikayya tsakanin kasashe.

  Alhaji Maikudi Gwarzo ya sanar da cewa duk mai kura da yadda al\’amura suke tafiya, zai amince cewa gwamnatin Buhari tana aiki bisa natsuwa da sanin ya kamata wajen aiwatar da dukkanin wasu manufofi da suka shafi rayuwar al\’umar kasa bisa yin la\’akari da bukatun kowane bangare.

  Sannan ya nunar da cewa duk kasar da ta rike noma da kiwo a matsayin babbar hanyar  kyautata tattalin arzikkn ta, ko shakka babu wannan kasa zata bunkasa cikin lokaci kankane, musamman ganin yadda ake samun amfanin gona mai yawa duk shekara, inda yayi  kira ga daukacin manoma dasu kara himma wajen aiki rani da damina domin samun rufin asiri ta fuskar wannan muhimmiyar sana\’a.

  A karshe, Alhaji Maikudi kura yayi amfani da wannan dama wajen yabawa gwamnatin Muhammadu Buhari saboda kokarin da take yi na kaucewa dogaro da man fetur a matsayin hanyar samun kudaden shiga zuwa fannin noma.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here