Magoya Bayan PDP Sun Yi Zanga-Zangar Haushin Zaben Fidda Gwani A Kaduna

  0
  439

  Daga Usman Nasidi

  MAGOYA bayan dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a Kaduna , Idris Mikati sun yi zanga-zangar nuna rashin jin dadin yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin a jihar.

  Masu zanga-zangar sun ce ba a yi adalci ba a zaben fidda gwani a Jihar Kaduna. Sun yi dandazo a sakateriyar jam’iyyar dake jihar, su na dauke da kwalaye da misalin karfe 11 na safe.

  Daga nan sai suka mika takardar korafin su ga sakataren jam’iyya na jiha. Sun dauki kimanin awa uku su na zanga-zangar nuna goyon Mikati.

  Sun yi zargin cewa an muzguna wa masu wakilan zabe kuma an yi amfani da kudi.

  Shugaban kungiyar masu goyon bayan Mikati, Albab Abdullahi, ya ce wanda suke goyon baya bai taba ficewa daga PDP ba.

  Sakataren jam’iyyar PDP Wosono ne ya karbe su kuma ya ce za a duba.

  A wani lamari na daban, mun ji cewa tsohon mataimakin kakakin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Comrade Timi Frank, ya yi watsi da ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke ci gaba da yi.

  Ya yi gargadin cewa su tabbatar da babu wani abu da ya samu tsohon gwamnan. Frank ya ce gargadin ya zama dole saboda bayanai da ya samu sun nuna cewa masu mulki sun umurci jam’iyyar da su bashi guba ko kuma su tagayyara shi gabannin zaben 2019.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here