Shugaba Buhari Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zantarwa A Fadar Villa

0
568

Daga Usman Nasidi

A RANAR Laraba 17 ga watan Oktoba na 2018, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jagoranci zaman majalisar zantarwa da aka saba gudanarwa cikin kowane mako a kasar nan.

An fara gudanar da wannan zama da misalin karfe 11.02 na safiyar yau ta Laraba yayin da shugaba Buhari ya isa farfajiyar taron a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na tarayya.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, karamin ministan makamashi, ayyuka da gidaje, Mustapha Shehuri, shine ya bude wannan taro da addu\’a tare da Ministan wasanni, Solomon Dalung.

Rahotanni sun bayyana cewa Ministan sadarwan nan da a halin yanzu rayuwa take masa kasa take dabo, Adebayo Shittu, na daya daga cikin kusoshin gwamnati da suka halarci zaman majalisar a garin na Abuja.

Hakazalika Minista Shittun na ci gaba da fuskantar yanayi na rayuwa na rashin samun tikitin takarar kujerar gwamnatin jihar Oyo da jam\’iyyar APC ta haramta masa a sanadiyar rashin yiwa kasa hidima ta hukumar NYSC da dokar kasa ta rataya bisa wuyan matasa.

Rahotannin sun kara da cewar cacar baki gami da nuna yatsa ta kaure tsakanin Sanatan jihar Kogi, Dino Melaye da kuma Sanatan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio kan tsarin zaman Sanatoci a majalisar dattawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here